Gwamnatin Gombe za ta ci gaba da biyan ’yan fansho – Zainab Haruna
A kokarin gwamnatin Jihar Gombe na faranta wa ma’aikatan da suka yi ritayashirye-shirye sun kammala don fara biyan tsofaffin ma’aikatan kudinsu na fansho.Babbar Sakatariya a Hukumar Fansho ta Jihar Hajiya Zainab I. Haruna ce ta bayyana hakan a Gombe, inda ta ce gwamnati ta ba da umarnin a ci gaba da biyan tsofaffin ma’aikatan da […]

A kokarin gwamnatin Jihar Gombe na faranta wa ma’aikatan da suka yi ritaya
shirye-shirye sun kammala don fara biyan tsofaffin ma’aikatan kudinsu na fansho.
Babbar Sakatariya a Hukumar Fansho ta Jihar Hajiya Zainab I. Haruna ce ta bayyana hakan a Gombe, inda ta ce gwamnati ta ba da umarnin a ci gaba da biyan tsofaffin ma’aikatan da suka yi ritaya a bara hakkokinsu.
A cewar Hajiya Zainab, ana sa ran za a fara biyan kudinsu na fansho a wannan mako, kuma kuma za a fara biyan kudin garatuti daga ranar 28 zuwa 30 ga watan Afrilun nan.
Babbar Sakatariyar ta shawarci dukkan ma’aikatan da suka yi ritaya cewa su kai je ofishin Baitumalin Jihar don karbar takardun shaidar da za a biya su kudadensu.