Gwamnatin Jigawa ta bankado ma’aikatan bogi 6,348

Ya ce an gano ma’aikatan bogi bayan tantancewa da gwamnatin ta gudanar.

Gwamnatin Jigawa ta bankado ma’aikatan bogi 6,348

Gwamnatin Jihar Jigawa, ta gano ma’aikatan bogi 6,348, yayin tantance ma’aikatan jihar, wanda hakan ya taimaka wajen hana zurarewar kudi sama da Naira miliyan 314 a wata da kuma Naira biliyan 3.7 a shekara.

Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Sagir Musa, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Dutse.

Ya ce an gano ma’aikatan bogi bayan tantancewa da gwamnatin ta gudanar ta hanyar daukar yatsunsu, wanda aka shirya domin tsaftace tsarin biyan albashi a jihar.

“A yayin gudanar da wannan bincike, an gano ma’aikata 6,348 na bogi, wanda hakan ya rage wa gwamnati asarar Naira 314,657,342 a wata da kuma kusan Naira biliyan 3.7 a shekara,” in ji Musa.

Ya bayyana cewa Majalisar Zartaswa ta Jihar, ta amince a kafa Cibiyar Tantance Ma’aikatan Jihar (CCC) a ofishin Shugaban Ma’aikatan Jihar.

“Wannan cibiya za ta taimaka wajen tantance tare da tallafawa tsarin domin tabbatar da ingantattun bayanan ma’aikata a nan gaba,” in ji shi.

Musa, ya kuma jaddada cewa wannan bincike na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na tabbatar da gaskiya da rikon amana a fannin ma’aikata.

Ya ce matakan da nufin hana hana sake samun matsalolin biyan albashin ma’aikata na bogi a nan gaba.

Kwamishinan ya bukaci ma’aikata da su bayar da hadin kai yayin ci gaba da aikin tantancewar.

Har ila yau, ya ce tsarin zai taimaka wajen mayar da kudade zuwa muhimman bangarori kamar ilimi, lafiya da gina ababen more rayuwa.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja