Gwamnatin Jigawa ta fara raba wa zawarawa bashin awaki
Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya fara cika alkawarin da ya dauka wa zawarawan jihar na ba su bashin awakin domin yin kiwo, wanda aka gudanar a garin Dutse fadar jihar a ranar Lahadin da ta gabata.Gwamna Badaru Abubakar ya ce kowace bazawara za a ba ta bashin awaki uku mata biyu da […]
Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya fara cika alkawarin da ya dauka wa zawarawan jihar na ba su bashin awakin domin yin kiwo, wanda aka gudanar a garin Dutse fadar jihar a ranar Lahadin da ta gabata.
Gwamna Badaru Abubakar ya ce kowace bazawara za a ba ta bashin awaki uku mata biyu da mace daya, inda ake sa ran za su fara biya bayan shekara biyu da karba, kuma kowace bazawara za ta mayar da awaki uku ne kamar yadda aka ba ta domin sauran zawarawa su samu ci moriyar shirin a nan gaba, shirin da ake sa ran zai hada da matan da ke yankunan karkara da biraren jihar.
A ranar kaddamar da shirin an raba wa mata 287 da suka fito daga kananan hukumomin masarautar Dutse a matsayin gwaji, inda ake sa ran shirin zai hade kananan hukumomin jihar 27.
Ana sa ran za a raba awaki dubu 17 ga zawarawan jihar, inda daga ciki aka bayar da 660 ga mata 220 da suka fito daga karamar Hukumar Gwaram.
Gwamna Badaru ya ce burinsu shi ne tallafa wa mata akalla dubu biyar don su ci moriyar shirin kiwon awakin na gwamnati. Ya ce hakan zai taimaka wa matan su zamo masu dogaro da kansu fiye da masu aikin gwamnati.