Gwamnatin Jigawa ta haramta wa mata, yara, tsofaffi zuwa sallar Idi
Gwamnatin jihar Jigawa ta haramta wa yara kanana da tsofaffi da mata zuwa sallar Idi a ranar Sallah. Gwamnatin ba ta tsaya nan ba, ta kuma haramta duk wasu bukukuwan Sallah da hawan Sallah ga sarakuna. Don haka ne ma gwamnatin ta umarci dukkan sarakuna su zauna a masarautun su. Bayanin hakan dai ya fito […]
Gwamnatin jihar Jigawa ta haramta wa yara kanana da tsofaffi da mata zuwa sallar Idi a ranar Sallah.
Gwamnatin ba ta tsaya nan ba, ta kuma haramta duk wasu bukukuwan Sallah da hawan Sallah ga sarakuna.
Don haka ne ma gwamnatin ta umarci dukkan sarakuna su zauna a masarautun su.
Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin gwamnan jihar, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar yayin wani taron manema labarai da ya kira ranar Talata a fadar gwamnatin jihar.
Da ya juya kan maganar karya dokar hana yawo da wasu suke yi a Dutse da daukacin kananan hukumomin da aka sanya dokar, ya ce gwamnatin jihar ta kafa kotunan tafi da gidanka domin hukunta duk wadanda aka kama domin hakan ya zame wa na baya darasi.
Game da jinyar wadanda suka kamu da cutar coronavirus kuwa, Gwamna Badaru ya ce gwamnati ta sanya gadaje 450 a dakunan killace mjinyata.
A cewar sa, a yanzu haka gwamnatin ta killace mutun 220 wadanda aka samu suna da cutar, ta kuma sallami mutun 71 wadanda suka warke.
Ya kara da cewa yanzu hakan shirye-shirye sun yi nisa na kafa cibiyar gwaji mallakar gwamnatin jihar domin gano masu dauke da kwayar cutar maimakon sai an kai samfur Kano ko Abuja.
Saboda haka ne ma gwamnan ya gargadi jama’ar jihar su kiyaye da dokokin da aka kafa na hana yawo da sanya kyallen rufe fuska don kare kansu daga kamuwa da cutar ta coronavirus.