Gwamnatin Jigawa ta kudiri aniyar hana bara
Gwamnatin Jihar Jigawa ta kudiri daukar matakin hana bara a daukacin fadin jihar a kokarinta na magance yawaitar barace-barace a titunan jihar baki daya.Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban karamar Hukumar Dutse da ke jihar Malam Abdul’aziz dankofa a lokacin da ake bikin raba zakka a masarautar Dutse a fadar Sarkin Dutse, inda […]

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kudiri daukar matakin hana bara a daukacin fadin jihar a kokarinta na magance yawaitar barace-barace a titunan jihar baki daya.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban karamar Hukumar Dutse da ke jihar Malam Abdul’aziz dankofa a lokacin da ake bikin raba zakka a masarautar Dutse a fadar Sarkin Dutse, inda ya ce tuni gwamnatin jihar ta raba wa kananan hukumomin jihar 27 da ke jihar sanarwa da nufin sanar da su cewa su hana bara a kowane sashi da ke yankunansu.
Ya kara da cewar sun sami sanarwa daga ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Lawan Abdu babura kan hakan, ya ce sana’ar bara tana zubar wa mutane mutunci a wajen sauran kabilun kasar nan. Ya ce abin kunya sai ka ga mutane suna bara a gidan mai ko wurin sayar da abinci ko maciya don wulakanta kai abin da ba za a ga sauran kabilu na yi ba.
Shugaban karamar hukumar ya nuna damuwa matuka game da yadda sana’ar bara take neman zama ruwan dare a jihar, kuma ya ce gwamnatin jihar ba za ta amince da yawan barace-barace a jihar ba, kuma duk wanda suka kama yana bara babu shakka za su gurfanar da shi a gaban kotu domin yin barar ya saba wa dokar gwamnatin jihar da ta kafa don ganin an hana bara a daukacin fadin jihar gaba daya.
Da yake jawabi Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi ya ce a wannan karo marasa karfi dubu 21 da 622 za su amfana da zakkar da aka tara daga wajan jama’a yayin da aka tara Naira miliyan 149 da dubu 582 da 593 da za a raba wa mabukata.