Gwamnatin Jigawa ta kulla alakar kasuwancin zovo-rodo da kasar Meziko
Gwamnatin Jihar Jigawa ta kulla huldar kasuwanci da kasar Meziko domin yin hada-hadar zovo a tsakaninsu. Hakan ya viyo vayan wata matsala da wasu ’yan kasuwa suka nemi vata wa jihar suna ne ta hanyar kai wani zovo marar inganci a kasar ta Meziko, lamarin da ya sa kasar ta hana a shigar mata da […]
Gwamnatin Jihar Jigawa ta kulla huldar kasuwanci da kasar Meziko domin yin hada-hadar zovo a tsakaninsu. Hakan ya viyo vayan wata matsala da wasu ’yan kasuwa suka nemi vata wa jihar suna ne ta hanyar kai wani zovo marar inganci a kasar ta Meziko, lamarin da ya sa kasar ta hana a shigar mata da zovo zuwa kasar daga Jihar Jigawa. Jihar ce ta fi dukan jihohin Najeriya noma zovo mafi inganci, kamar yadda Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa varista Ivrahim Hassan Hadeja ya shaida wa manema lavarai a ranar Talatar makon jiya.
Alhaji Ivrahim Hassan Hadeja ya ce yanzu haka gwamnatin jihar da Hukumar Tantance Ingancin Avinci da Magunguna ta kasa (NAFDAC) sun zauna a kan tevurin shawara domin nema wa kasuwar zovo farin jini tare da nemo hanyoyin da za a inganta harkokin noman zovo a jihar ta Jigawa.
Yana mai cewa nan gava kadan gwamnatin jihar za ta shirya gangamin wayar da kai domin fadakar da manoman jihar ta Jigawa kan yadda za su inganta harkokin noman zovo a jihar, tare da koya wa manoma davarun harkokin kasuwancin zamani domin su rika samun riva mai yawan gaske wajen dogara da kansu.
Ya kara da da cewa gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar hukumar tantance ingancin avinci da ake fita da shi da wadda ake shigowa da shi kasar nan za su kafa civiyoyin tavvatar da ingancin kayan da ake shigowa da fita da su daga Najeriya a civiyar kasuwanci da ke Maigatari da kuma karamin ofishinsu da ke karamar Hukumar Taura. Haka nan kuma hukumar za ta samar da ofishin vavvan jami’inta a virnin Dutse domin gudanar da ayyukansu a jihar ta Jigawa