Gwamnatin Jigawa ta samar da tuka-tuka 180 da sola 17 a Kafin Hausa

Gwamnatin Jihar Jigawa ta tona tuka-tuka 180 tare da fanfuna 17 masu aiki da hasken rana a yankin karamar Hukumar Kafin Hausa da ke jihar.dan Majalisar Jihar mai wakiltar mazabar Kafin Hausa Malam Abdulwahab Muhammed Suleiman Toro ne ya shaida wa  wakilinmu haka a lokacin da suke zantawa a makon jiya. dan Majalisa Abdulwahab Toro ya […]

Gwamnatin Jigawa ta samar da tuka-tuka 180 da sola 17 a Kafin Hausa
Gwamnatin Jigawa ta samar da tuka-tuka 180 da sola 17 a Kafin Hausa

Gwamnatin Jihar Jigawa ta tona tuka-tuka 180 tare da fanfuna 17 masu aiki da hasken rana a yankin karamar Hukumar Kafin Hausa da ke jihar.
dan Majalisar Jihar mai wakiltar mazabar Kafin Hausa Malam Abdulwahab Muhammed Suleiman Toro ne ya shaida wa  wakilinmu haka a lokacin da suke zantawa a makon jiya.
 dan Majalisa Abdulwahab Toro ya ce jama’ar Kafin Hausa da kewaye gaba dayansu babu  abin da za su ce a kan wannan gwamnati mai ci ta Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar sai godiya, ba don komai ba sai domin  a lokacin gwamnatin da ta shude, jama’ar yankin sun sha bakar wahala saboda babu abin da gwamnatin baya ta yi wa jama’ar yankin.
Ya kuma kara da cewa zuwansa Majalisar Dokoki ta Jihar Jigawa ta sa jama’ar yankin sun fuskanci akwai sauyi mai ma’ana, domin yanzu haka gwamnatin jihar tana yin ayyuka a daukacin mazabun yankin 113 domin inganta rayuwar jama’ar yankin kuma kowa ya san gwamnatin jihar tana damawa da su.
Ya shawarci jama’ar yankin Kafin Hausa su ci gaba da yi wa Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar addu’a a kan irin ayyukan alheri da gwamnatinsa ta sanya a gaba don ganin jama’a sun amfana, kuma ya nemi jama’ar jihar su ci gaba da ba su hadin kai da goyon baya domin ganin hakarsu ta cimma ruwa na taimaka wa gwamnatin ta samu nasara.