Gwamnatin Jigawa za ta dawo da ‘Yan Akwati domin zaven 2019
Gwamnatin Jahar Jigawa za ta dawo da kudaden akwati domin amfani da su wajen yakin neman zave, wannan yana daya daga cikin tsarin siyasa irin na tsohon gwamnan Jahar Jigawa, Alhaji Ibrahim Saminu Turaki. Wadda ita a yanzu wannan gwamnatin maimakon ‘yan goma da tsohuwar gwamnatin Saminu ta yi, ita za ta yi amfani da […]

Gwamnatin Jahar Jigawa za ta dawo da kudaden akwati domin amfani da su wajen yakin neman zave, wannan yana daya daga cikin tsarin siyasa irin na tsohon gwamnan Jahar Jigawa, Alhaji Ibrahim Saminu Turaki. Wadda ita a yanzu wannan gwamnatin maimakon ‘yan goma da tsohuwar gwamnatin Saminu ta yi, ita za ta yi amfani da ‘yan 40 a matsayin wakilanta a daukacin mazavu dake kananan hukumomin jahar 27 da nufin su ne za su yi mata yakin neman goyan bayan jama’a.
Vullar labarin hakan ya fito ne a daidai lokacin da shugaban Jam’iyyar APC ta mata ta kai ziyara karamar Hukumar Gwiwa take bayyana haka a dakin taro na karamar hukumar ga taron shugabanin jam’iyya data bukaci shugaban karamar hukumar hukumar ta Gwiwa da ya tara mata.
Ta ce gwamnatin jahar za ta yi amfani da ‘yan 40 wajen yakin neman zave a 2019, ta kara da cewar yanzu haka suna da ‘yan 30 wadda maza 20 mata 10 kuma akwai ‘yan 20 da za su ci moriyar shirin su ma, gwamnatin jahar za ta cika masu alkawarin da ta dauka tun lokacin yakin neman zave a 2015.
Hajiya Binta Farin Dutse wadda ita ce shugabar mata ta jam’iyyar APC a Jahar Jigawa, ta nemi wadanda aka vatawa a baya da su yi hakuri kuma su tsaya tsayin daka wajen marawa gwamnatin jahar ta Jigawa baya, domin ganin Gwamna Badaru ya sake darewa gadon mulki karo na biyu a jahar.
Hajiya Binta ta kuma nuna takaicinta game da yadda aka yi watsi da ‘yan jam’iyya, dan haka ta ba su tabbacin cewar gwamnati za ta ci gaba da da tafiya da kowa, sannan ta gargadi sauran ‘yan jam’iyya da su guji nunawa wadanda suka dawo cikin jam’iyyar bambanci. Ta na mai cewa su daina nuna masu kyama saboda dama tare suke tafiya kawai suka yi yanzu dan sun dawo gida bai kamata ace ana nuna masu bambanci ba, ta kuma hore su da su hada kansu wajen yi wa jam’iyyar aiki a gudu tare a tsira tare.
Ta kuma kara da cewar suna nan tafe wajen dawowa karamar hukumar za su amshi bashin da suka bawa mata na kiwon awaki domin wasu su amfana, ta ce gwamnati ba za ta amince da bayanan boge ba, dole ne sai sun ga bayanai a rubuce duk wadda bai sanar da karamar hukuma ba, wata matsala akan akuyar da aka ba shi sai yanzu ya zo haka da baki ya ce ta mutu, ba makawa sai ya biya bashin.
Shi ma da yake nasa jawabin, Shugaban karamar Hukumar ta Gwiwa, Abdullahi Idris Daurawa ya ce duk wadanda aka bawa bashin awaki suka mutu, sun dauki sunayensu, domin bin ka’ida, haka zalika duk wadanda suke da wata matsala akan awakin an dauki sunayensu kuma wadanda suka biya bashin an dauki jadawalin sunayensu komai yana cikin tsari.