Gwamnatin Jigawa za ta dinka wa dalibai mata 13,500 yunifom
Gwamnatin Jihar Jigawa za ta dinka wa daliban manyan makarantun sakandare yunifom kyauta.Kwamashinan Watsa Labarai na Jihar, Alhaji Bala Ibrahim Mamsa ya fada wa manema labarai haka bayan taron Majalisar Zartawar Jihar da aka yi a gidan gwamnati.Ya ce gwamnatin jihar za ta kashe Naira miliyan 77 da dubu 900 wajen dinka wa dalibai dubu […]
Gwamnatin Jihar Jigawa za ta dinka wa daliban manyan makarantun sakandare yunifom kyauta.
Kwamashinan Watsa Labarai na Jihar, Alhaji Bala Ibrahim Mamsa ya fada wa manema labarai haka bayan taron Majalisar Zartawar Jihar da aka yi a gidan gwamnati.
Ya ce gwamnatin jihar za ta kashe Naira miliyan 77 da dubu 900 wajen dinka wa dalibai dubu 13 da 500 na manyan makarantar sakandare yunifon guda bibbiyu, kuma za a raba wa daliban kayan ne kyauta inji kwamashinan Sai ya ce gwamnatin jihar ta kwace wasu ayyukan kwangila na gyare-gyaren magudanun ruwa da titunan cikin gari da ba a kamala ba, inda ta sake bayar da ayyukan ga wasu kamfanoni domin ci gaba da ayyukan.