Gwamnatin Jigawa za ta kafa masaka da kamfanin tumatir

Shirye shirye sun kankama don kafa masaka ta zamani a Jihar Jigawa  lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta gayyato kwararru daga kasar China tare da hadin gwiwar ’yan kasuwar gida domin ganin an kafa masakar mai suna ‘Nice Garment’ a jihar. Gwamnan Jihar Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya shaida wa manema labarai haka a […]

Gwamnatin Jigawa za ta kafa masaka da kamfanin tumatir

Gwamna Muhammad Abubakar Badaru na Jihar Jigawa

Shirye shirye sun kankama don kafa masaka ta zamani a Jihar Jigawa  lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta gayyato kwararru daga kasar China tare da hadin gwiwar ’yan kasuwar gida domin ganin an kafa masakar mai suna ‘Nice Garment’ a jihar.

Gwamnan Jihar Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya shaida wa manema labarai haka a ranar Talatar da ta gabata,  inda ya cew za a kashe kimanin Dala miliyan 120 wajen gina masakar kuma tuni aka yi odar manyan injina daga kasar China da za a kafa domin masakar ta fara aiki.

Ya ce ana sa ran matasa sama da dubu 60 za su samu aikin yi da zarar masakar ta fara aiki ya kuma yi alkawarin gwamnatin jihar za ta samar da ruwan sha da kula da tsaro da lura da yadda za a ci gaba da samun zaman lafiya mai dorewa a jihar.

Gwamna  Badaru ya ce ba komai ya sa baki suke sha’awar shigowa jihar su kafa masana’antu ba illa zaman lafiya da jihar take da shi .

Ya ce gwamnati za ta yi kokari ganin an samar da wadatattun kamfanoni a jihar domin matasa su zama masu dogaro da kansu, inda ya ce yanzu haka shirye-shiye sun yi nisa wajen kafa kamfanin tumatir a Karamar Hukumar Birniwa.

Ya ce “Wadanda suke haya da babura da Gwamnatin Jihar Legas ta koro su zuwa gida za mu tantance su domin sama musu aiki a kamfanin tumatir da ake sa ran zai fara aiki kwanan nan domin su samu abin yi su daina zuwa ci-rani Kudancin Najeriya.”