Gwamnatin Jigawa za ta kashe Naira miliyan 14 a gasar karatun Alkur’ani ta bana

A watan nan na Nuwamba da muke ciki ake sa ran fara gasar karatun kur’ani ta bana a matakin jiha, karo na 32 a Jihar Jigawa, inda ake sa ran kashe Naira miliyan 14 domin gudanar da gasar; a kokarin jihar na samar da zakaru a fagen gasar domin fafatawa da takwarorinsu da ke sauran […]

Gwamnatin Jigawa za ta kashe Naira miliyan 14 a gasar karatun Alkur’ani ta bana

A watan nan na Nuwamba da muke ciki ake sa ran fara gasar karatun kur’ani ta bana a matakin jiha, karo na 32 a Jihar Jigawa, inda ake sa ran kashe Naira miliyan 14 domin gudanar da gasar; a kokarin jihar na samar da zakaru a fagen gasar domin fafatawa da takwarorinsu da ke sauran jihohin kasarnan da za a yi nan gaba.

Ustaz Yakubu Abbas Yakubu ne ya sanar da taron manema labarai haka a ranar Litinin da ta gabata a ofishinsa. Ya kara da cewa a yayin gasar, kananan hukumomin jihar guda 27 gaba daya za su shiga gasar kuma ana sa ran dalibai 324 za su shiga domin a fafata da su, domin a samu zakarun da za su wakilci jihar a matakin gasar na kasa, a bana.

Ya ce a yayin gasar, za a yi gudanar da ita ne a kan Izifi goma da Izifi 20 da kuma matakin Izifi 30 da Izifi 40, hakazalika akwai wadanda za su fafata a kan Izifi 50 da Izifin karshe wato na 60, domin ganin an sami zakarun a kan matakai daban-daban.

“Tuni gwamnatin jiha ta ware Naira miliyan 14, domin tunkarar shirin gasar ta bana. Za mu yi amfani da kudin wajan daukar nauyin alkalai masu lura da gasar da dawainiyar dalibai tare da sayen kayan da za a ba wadanda suka yi hazaka kyauta da kuma kulawa da lafiyar daliban da abicin da za su ci a masaukansu, a yayin zaman masabakar ta bana,” inji shi.

Ya kara da cewa alkalan masabakar shida ne aka gayyata, wadanda kwararru ne a fagen alkalancin masabaka ta kasa da ma duniya, wadanda gwamnatin jihar ta amince da su, a matsayin wadanda za su yi alkalanci a wajen gasar ta bana.