Gwamnatin Jigawa za ta raba injin ban-ruwa ga manoma
Hukumar Bunkasa Aikin Gona ta Jihar Jigawa (JASCO) ta sayo injunann ban-ruwa masu aiki da hasken rana guda 100 a kan Naira miliyan 55 don raba wa manoma bashi da nufin inganta noman rani a jihar. Mukaddashin Manajan Daraktan Hukumar JASCO, Malam Muhammad Lano ya bayyana haka, inda ya ce hukumar ta sayo taraktocin noma […]
Hukumar Bunkasa Aikin Gona ta Jihar Jigawa (JASCO) ta sayo injunann ban-ruwa masu aiki da hasken rana guda 100 a kan Naira miliyan 55 don raba wa manoma bashi da nufin inganta noman rani a jihar.
Mukaddashin Manajan Daraktan Hukumar JASCO, Malam Muhammad Lano ya bayyana haka, inda ya ce hukumar ta sayo taraktocin noma guda 100 da kowace daya a kan Naira miliyan 6.5, da ake ba wa manoma bashi da nufin a taimaka wa manoman jihar ta fuskar aikin gona.
Sai dai ya koka kan yadda aka samu bullar kwari masu lalata ridi da sauran kayan amfanin gona a sassan jihar, sannan ya ce yanzu haka sun samar da magungunan feshin kwari da za su kashe kwarin masu lalata kayan gona domin sayar wa manoma a farashi mai sauki.
Ya kara da cewa sakamakon bullar kwarin ne Gwamnatin Jihar ta sayo maganin kashe kwarin na Naira miliyan 12.2 da nufin kawo karshen matsalar da ta addabi manoma a jihar.