Gwamnatin Jigawa za ta raini irin itatuwa dubu 90 bana

Sashin Raya Gandun Daji na Jihar Jigawa zai raini itatuwan darbejiya da turare da keshiya dubu 90 a bana. Daraktan Gandun Daji na Jihar, Malam Sunusi Yakubu Babura ne ya bayyana haka a hirar da ya yi da Aminiya, inda ya ce suna rainon itatuwan ne a Hadeja da Ringim inda suke rainon itatuwa dubu […]

Gwamnatin Jigawa za ta raini irin itatuwa dubu 90 bana
Gwamnatin Jigawa za ta raini irin itatuwa dubu 90 bana

Sashin Raya Gandun Daji na Jihar Jigawa zai raini itatuwan darbejiya da turare da keshiya dubu 90 a bana.

Daraktan Gandun Daji na Jihar, Malam Sunusi Yakubu Babura ne ya bayyana haka a hirar da ya yi da Aminiya, inda ya ce suna rainon itatuwan ne a Hadeja da Ringim inda suke rainon itatuwa dubu 60. Sun kuma raini itatuwan zogale da turare da darbejiya da malaina da sauransu.

Sunusi Babura ya kara da cewa sun rani itatuwan gwaiba da gwandar Masar da sauran itatuwa 2,500, sai dai ya koka game da karancin itatuwan da suka dasa a bana.  Ya ce yanzu haka akwai makarantu da suke bukatar itatuwan, amma babu isassu da za su dasa.

Ya ce, sun ware irin itatuwan da za su raba wa makarantu da asibitoci a jihar da nufin bunkasa lafiyar yara da mata masu juna biyu.

Daraktan ya ce ba za su zuba ido suna kallo wadansu batagari suna lalata dazuzzuka ba, kuma duk wanda suka kama yana satar bishiya ko yanyanke ta zai fuskanci fushin hukumar.

Ya ja hankalin jama’a su guji sare itatuwa ba tare da izinin hukuma ba, inda ya ce yawan sare itatuwan ne kan gaba wajen lalacewar yanayi da kwararowar hamada wadda take barazana tare da lalata gandun daji a jihar.