Gwamnatin Jihar Bauchi ta ba nakasassu kayan abinci buhu dubu 10

Gwamnain Jihar Bauchi ta ba nakasassu tallafin kayan abinci buhu dubu 10 domin rage musu wahalhalun da suke fuskanta a rayuwa.Da yake mika kayan abincin a ofishinsa, Mai tallafa wa Gwamnan Jihar kan harkar ciyar da nakasassu Alhaji Salisu Garba Maisuga ya ce wannan hakki ne da Gwamna ya dora masa don ciyar da nakasassun […]

Gwamnatin Jihar Bauchi ta ba nakasassu kayan abinci buhu dubu 10
Gwamnatin Jihar Bauchi ta ba nakasassu kayan abinci buhu dubu 10

Gwamnain Jihar Bauchi ta ba nakasassu tallafin kayan abinci buhu dubu 10 domin rage musu wahalhalun da suke fuskanta a rayuwa.
Da yake mika kayan abincin a ofishinsa, Mai tallafa wa Gwamnan Jihar kan harkar ciyar da nakasassu Alhaji Salisu Garba Maisuga ya ce wannan hakki ne da Gwamna ya dora masa don ciyar da nakasassun kuma a duk lokacin da aka ga abin da bai dace ba a fadakar da su.
Alhaji Salisu Maisuga ya ce gwamnati na bayar da wannan taimako ne don rage wahalhalu ga nakasassun inda duk bayan wata hudu ake ba su wannan tallafi saboda irin gudunmawar da suke bayarwa ga zaman lafiya a jihar da kasa baki daya. Ya ce a kullum ana kara yawan wannan agaji saboda wanda aka bayar a watan Yuli buhu dubu tara ne, kuma ana zaton a wata hudu masu zuwa za a sake kara yawan tallafin.
Sarkin Makafin Jihar Bauchi Alhaji Abdullahi Jibrin ya gode wa Gwamna Isa Yuguda kan taimakon kayan abinci da ya raba musu sau uku a shekara, inda ya bayyana lamarin a matsayin aikin da ke taimakawa wajen rage yawon bara a tsakanin nakasassu a fadin jihar.
Alhaji Abdullahi Jibrin ya ce musakai a jihar a kowace Juma’a suna hada kansu don yi wa jihar da kasa addu’o’in fatar alheri da neman zaman lafiya, “Fadar Sarkin Makafi kan tara alarammomin makafi har ma da almajirai masu ido ana saukar alkur’ani sau 12 duk Juma’a, haka Sarkin Kutare da Sarkin Guragu da Sarkin Kurame suke yi a duk mako. Kuma muna samun tallafi daga Gwamna Yuguda da wasu kwamishinoni da suke agazawa don gudanar da wannan aiki,” inji shi.
Ya yi tir da yunkurin hana bara da wasu jihohi ke yi, inda ya ce su ma ba sa jin dadin yin barar ya zamo dole ne saboda su samu abin da za su ci da iyalansu, “amma idan mutum ya matsa mun zuba wa Allah ido don Shi ne shugaban masu mulki,” inji shi.
 Sarkin Kutaren Bauchi Malam Zakari Ya’u Bala da Sarkin Guragu Malam Abubakar Bello su ma sun yaba da wannan taimako tare da alkawarin za su raba bil hakki da gaskiya.
Sakataren hadakar kungiyar nakasassu ta Jihar Bauchi Alhaji Tata Gurgu Ningi ya roki gwamnatin jihar da ta tarayya su fito da shirin ba da ilimi kyauta ga ’ya’yan nakasassu tun daga firamare har zuwa jami’a don inganta rayuwarsu.