Gwamnatin Jihar Filato ba ta tallafa wa ’yan kasuwa -Ibrahim Inusa

Shugaban kasuwar ‘yan kabeji da ke Farar-gada a garin Jos, babban birnin Jihar Filato, Malam Ibrahim Inusa, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Filato da kananan hukumomin jihar ba sa tallafa wa ‘yan kasuwar jihar, kamar yadda ake tallafa wa ‘yan kasuwa a wasu jihohin kasar nan. Malam Ibrahim Inusa ya bayyana haka ne a lokacin […]

Gwamnatin Jihar Filato ba ta tallafa wa ’yan kasuwa -Ibrahim Inusa
Gwamnatin Jihar Filato ba ta tallafa wa ’yan kasuwa -Ibrahim Inusa

Shugaban kasuwar ‘yan kabeji da ke Farar-gada a garin Jos, babban birnin Jihar Filato, Malam Ibrahim Inusa, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Filato da kananan hukumomin jihar ba sa tallafa wa ‘yan kasuwar jihar, kamar yadda ake tallafa wa ‘yan kasuwa a wasu jihohin kasar nan. Malam Ibrahim Inusa ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce a wasu jihohin kasar nan za ka ga gwamnati tana tallafa wa ‘yan kasuwa ta hanyar ba su rancen kudi domin su yi jari, tare da gyara masu kasuwannin da suke kasuwanci, amma mu ‘yan kasuwa Jihar Filato ba a yi mana komai.
Ya ce misali kamar a kasuwarmu ta ‘yan kabeji babu wani abu da gwamnati ta taba yi mana a cikin wannan kasuwa. Ya ce a wannan kasuwa babu hanyar shigowa, babu ruwan sha, babu wurin bayan gida. Ya ce mun sha kai kukanmu ga gwamnatin karamar hukumar Jos ta Arewa da gwamnatin jiha, amma babu abin da ya gudana.
Malam Ibrahim Inusa ya yi bayanin cewa a bangarenmu na ‘yan wannan kasuwa, mun yi abubuwa da dama a cikin kasuwar da suka hada da gina gidan wanka da gina hanyar ruwa da yin cikon kasa a cikin kasuwar, tare da jawo wutar lantarki zuwa cikin kasuwar.
Don haka ya yi kira ga gwamnatin Jihar Filato da karamar hukumar Jos ta Arewa kan su tallafawa wannan kasuwa ta ’yan kabeji. Ya ce a duk jihar Filato babu kasuwar da take samun baki daga kowanne bangare na kasar nan, da suke kawo kayayyakin lambu tare sayen kayayyakin kamar wannan kasuwa ta ‘yan kabeji.
Ya ce duk rikice rikicen da aka yi a garin Jos a baya, ba su taba samun wata damuwa ba a wannan kasuwa, domin a wannan kasuwa Allah ya ba su hadin kai a tsakanin Musulmi da Kirista da ma wanda ba shi da addini suna zaune lafiya.