Gwamnatin Jihar Jigawa ta ba dangote filin noma rake

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ba Kamfanin dangote Group hekta dubu 2 domin noma rake, sakamakon kokarinsa na kafa kamfanin yin sukari a jihar.Kwashinan Aikin Gona na Jihar Jigawa, Alhaji Rabi’u Isah Raura ne ya ce hakan bayan ya kira taron ’yan jarida a ranar Talata.Ya ce gwamnati ta samar da shanun noma 2,500 don inganta […]

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ba dangote filin noma rake
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ba dangote filin noma rake

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ba Kamfanin dangote Group hekta dubu 2 domin noma rake, sakamakon kokarinsa na kafa kamfanin yin sukari a jihar.
Kwashinan Aikin Gona na Jihar Jigawa, Alhaji Rabi’u Isah Raura ne ya ce hakan bayan ya kira taron ’yan jarida a ranar Talata.
Ya ce gwamnati ta samar da shanun noma 2,500 don inganta harkar noma  a Jihar Jigawa.
Ya ce: “A yanzu mun kammala shirye-shiryen fara yin sukari a Jihar Jigawa. Hakan ya sa muka ba Kamfanin dangote hekta dubu 2, inda a shekara mai zuwa za a fara samar da sukarin.”
“Mun kuma samar da shanu 2,500 don tallafa wa manoma, sannan mun sayi takin zamani kimanin tan 6,000, wadda za mu raba wa manoma a bana.” Inji Raura.
A karshe ya ce gwamnati za ta samar da fanfunan ruwa masu aiki da iska (windmill) 80 ga makiyaya a kokarin gwamnati na magance rikici tsakanin manoma da makiyaya.