Gwamnatin Jihar Kaduna ba ta tallafa wa wasannin guragu yadda ya dace -Bello dan Auta
Wani gurgu da ake kira Bello dan Auta ya koka a kan yadda Gwamnatin Jihar Kaduna ba ta ba nakassu gudunmawar da ta dace musamman wadanda ke buga kwallon guragu da aka fi sani da “Para-Soccer”. Ya ce abin bakin ciki ne yadda wasan yake kankama a wasu jihohi musamman wadanda ke Kudancin kasar nan […]
Wani gurgu da ake kira Bello dan Auta ya koka a kan yadda Gwamnatin Jihar Kaduna ba ta ba nakassu gudunmawar da ta dace musamman wadanda ke buga kwallon guragu da aka fi sani da “Para-Soccer”. Ya ce abin bakin ciki ne yadda wasan yake kankama a wasu jihohi musamman wadanda ke Kudancin kasar nan amma sai aka samu koma baya a Jihar Kaduna.
Bello Dan Auta ya ce ya fara wannan wasan ne bayan ya ga wani amininsa mai suna Mustapha suna wasa a filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna kimanin shekaru goma sha shida da suka wuce. Ya fara koyon wasan ne kamar yadda sauran suke yi da yamma. Inda sabon shiga ake sa shi ya kalli yadda ake buga wassan da kula da tsare dokokin wasan kafin a fara sa shi cikin kwararru.
Yace ya dau tsawon shekara guda kafin ya kware inda ya hada da kallon wasannin kwallon kafa na kwararru a talbijin. Akan yadda ya zama yanzu har yana horar da wasu, sai ya ce ko gurgu ko mutum mai kafafu yana iya yin alkalin wasan wanda dokokin sa iri daya ne da na kwallon kafa.
A dangane da yadda suke samun katakon takalmin-tayan da suke zama akai don yin wasa sai ya ce suna sayen takalmin taya ne sannan su yanke takalmin sai su dora katako a kai sannan su sa bel su daure kafafunsu don su yi wasa a kai. Ana sayen takalmin-tayan ne a kan Naira 2,500 zuwa Naira 5,000. Wani lokaci suna sayen takalmin guda biyu ne don ‘yan kasuwan ba sa sayar musu da kafa daya sai dai biyu.
Bello danAuta yace ya buga gasa iri-iri don wakiltar jihar Kaduna har a gasar wasanni na kasa. Ya ce kocin jihar Kaduna na farko shi ne Malam Yusuf Pate Bamalli wanda ya kambama wasan inda ya kai ‘yan wasa har garuruwan Legos da kuma Abuja.
Ya kara da cewa gwamnatin Jihar Kaduna da ma’aikatar wasanni sun ba su wurin wasa ne a dandalin Murtala Muhammad da ke Kaduna. Kuma in ba motar da ke jigilar su zuwa gasa ba, gwamnatin jihar ba ta tallafa musu da alawus, ko kayan wasa, ko rigunan wasa da dai sauransu. Suna yin komai ne aljihunsu don bayar da gudunmawarsu ga cigaban jihar amma kuma aka yi biris da su. Ya ce ba su da kudi don a wani lokaci in sun haralci gasar guragu haka suke kula da kansu da kansu ba tare da wani tallafi daga gwamnatin jiha ba.
Ya ce ya ziyarci Jihohin Legas da Kano da kuma Filato a wajen halartar gasannin guragu daban-daban na kasa. Yanzu dai Bello dan Auta ya kasance yana yin alkalanci a wasan guragu ne da kuma horarwa.