Gwamnatin Jihar Legas na feshin yakar zazzabin cizon sauro

Mutanen da yawansu ya kai miliyan 3 da rabi ne gwamnatin Jihar Legas ta yi nasarar yi wa feshi a yankinsu don samun kariya  daga zazzabin cizon sauro a shekarar da ta gabata, a karkashin shirin feshin maganin kwari  da ta gudanar gida-gida. Kwamishinan kiwon lafiya na  jihar,  Dokta Jide Idris shi ne ya bayyana […]

Gwamnatin Jihar Legas na feshin yakar zazzabin cizon sauro

Mutanen da yawansu ya kai miliyan 3 da rabi ne gwamnatin Jihar Legas ta yi nasarar yi wa feshi a yankinsu don samun kariya  daga zazzabin cizon sauro a shekarar da ta gabata, a karkashin shirin feshin maganin kwari  da ta gudanar gida-gida.
Kwamishinan kiwon lafiya na  jihar,  Dokta Jide Idris shi ne ya bayyana hakan sa’ilin da yake wa taron manema labarai jawabi jim kadan kafin a fara wani sabon shirin feshin na gida-gida.
Dokta Idris ya ce a bara an yi feshin ne a kananan hukumomi 13. Daga  shekarar  2001 ce  dai aka fara wannan shirin, wanda gidaje 49,003 suka amfana. Akan yi feshin ne a bangwaye da kuma cikin rufin daki inda sauro da sauran kwari ke makalewa domin kashe su kuma a hana su yaduwa.
Kwamishinan  ya ce gwamnati  ta samar da  shirin ne domin rage yawan  yaduwar  sauro, lamarin da zai sa a rage  yawan kamuwa  da zazzabin cizon sauro, domin ba Jihar Legas ba,  a daukacin Najeriya, cizon  sauro ya zame barazana  ga  jama’a, shi ya sa  gwamnati  tabullo  da  shirin kuma  ana  samun nasara  bakin gwargwadon hali.
Dokta Idris ya ce wannan shekarar za a  yi a kananan hukumomi 6  da  kuma duk yankunan  raya  karkara da  suka  fada  cikin  wadannan   kananan hukumomin, kodayake za  a mayar  da  hanklali a kananan hukumomin Ikorodu  da Ibeju Kekki saboda bincike ya nuna su ne  suka  fi  yawan samun  barazanar  cizon  sauro idan an kwatanta su da  auran.
Kwamishinan ya ce shirin yana cikin shawarwarin da hukumar lafiya ta duniya ta bayar kuma gwamnatin Jihar Legas ce  kawai ta fara aiwatar da shi a Najeriya, saboda haka ne ma ya yi kira  ga  magidanta su hada kai da masu aikin feshin, musamman ta fuskar lullube kowane abinci ko na sha da kyau.
Ana sa ran za a yi kwanaki 40 ana gudanar da aikin, wanda ba a karbar ko sisin-kwabo hannun kowa.