Gwamnatin Jihar Legas za ta hana shan sigari

Kwanan nan gwamnati Jihar Legas za ta shiga hukunta duk wanda ta samu yana zukar tasba sigari a matattarar jama’a, domin majalisar dokokin jihar ta kammala dokar zuwa matakin karatu na  3, saboda haka ana jira Gwamna Babatunde Raji Fashola ya sa hannu.Da zarar dokar ta fara aiki, za a hana shan sigari a wurare […]

Gwamnatin Jihar Legas za ta hana shan sigari
Gwamnatin Jihar Legas za ta hana shan sigari

Kwanan nan gwamnati Jihar Legas za ta shiga hukunta duk wanda ta samu yana zukar tasba sigari a matattarar jama’a, domin majalisar dokokin jihar ta kammala dokar zuwa matakin karatu na  3, saboda haka ana jira Gwamna Babatunde Raji Fashola ya sa hannu.
Da zarar dokar ta fara aiki, za a hana shan sigari a wurare kamar su asibiti da tashar mota da dakunan karatu da wajen  renon yara da dakunan sayar da  abinci ko kuma cikin motar  fasinja  da  dai  duk  wani  wuri  da yake matattarar jama’a ne.
Dokar  za ta kunshi  sassa 16, wadanda suka hada da hana sa allon sanarwa da ke tallata taba sigari, da hana sa tallar taba a  kwalin tabar; haka  kuma  duk wuraren da aka hana shan tabar, za a sa sanarwa ba a shan taba a wannan wurin. A sashe  na 4 na dokar, za a tilasta  duk wani  mai  daya daga  cikin  wadannan wuraren da aka  hana shan sigari, ya sa  babban allon sanarwar hana shan taba, wanda rashin  yin haka  shi ma wani laifi ne.
Hukuncin wanda aka kama da karya  wannan dokar shi ne biyan tarar Naira dubu 10  ko kuma daurin wata 1 ko kuma  watanni 3 ko kuma duka biyu. Haka  kuma  wanda  aka  gurfanar  kan  laifin a karo na  biyu, zai fuskanci tarar Naira dubu 50 ko kuma daurin watanni  3 gidan yari. Shi ma wanda ya ki sa sanarwar ba a shan taba, zai fuskaci tarar Naira dubu 100 ko kuma daurin  watanni 6 a gidan yari.
Haka  kuma wanda ya  zuki  sigari  gaban karamin yaro har aka kama shi  zai  biya  tarar  Naira dubu 15 ko kuma ya yi  zaman gidan yari  na tsawon watanni 3, shi ma wanda ya hana jami’an tsaro ko kuma  jami’i  hana shan sigari  cikin jama’a, ya aikata babban laifi, kuma zai fuskanci  hukunci.
Dokar  za ta  fara  aiki ne  nan take  da  zarar  gwamna  ya sa   mata  hannu.