Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bayar da hayar mayankarta
Gwamnatin Jihar Sakkwato, karkashin jagorancin Alhaji Aliyu Wamakko ta bayar da hayar mayankar dabbobi mallakar jihar na tsawon shekara biyu kan kudi Naira miliyan 120 ga wani kamfani mai suna Gidan Haki. Wannan bayani ya fito ne daga bakin Kwamishinan Kula Da Kiwon Dabbobi Da Kifaye na jiha, Alhaji Garba Nomau Sanda, a zantawarsa da […]
Gwamnatin Jihar Sakkwato, karkashin jagorancin Alhaji Aliyu Wamakko ta bayar da hayar mayankar dabbobi mallakar jihar na tsawon shekara biyu kan kudi Naira miliyan 120 ga wani kamfani mai suna Gidan Haki.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Kwamishinan Kula Da Kiwon Dabbobi Da Kifaye na jiha, Alhaji Garba Nomau Sanda, a zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar zartawa ta jiha da aka yi a fadar gwamnati a Larabar da ta gabata.
Alhaji Garba ya ci gaba da cewa: “Wannan kamfanin shi ne wanda ya gyara mayankar ta dawo ta zamani, sabanin inda aka fito, kan hakan ne gwamnati ta yi shawarar abin da zai kara bunkasa tattalin arzikin wannan jiha kuma mahautar ingancinta ya dore; aka ga ba wani abu da zai kawo haka sai a damka wa wannan kamfani amanar mayankar na shekara goma amma a fara da shekara biyu don kowace shekara za a samu karin miliyan 10 bayan biyun farko.”
Ya cigaba da cewa: “Wannan yarjejeniya aminci ne tsakanin gwamnati da kamfanin domin bunkasa tattalin arzikin jihar, ta hanyar fadada kudin shiga. A shekara goma, gwamnatin jiha za ta samu Naira miliyan 680 ta wannan mayankar.”
Haka ma Kwamishinan Kudi na jiha, Alhaji Isah Bajini ya bayyana kasafin kudin da gwamanatin jihar za ta mika wa majalisar wakilai na wannan shekara ta 2014, wato sama da Naira biliyan 112, sabanin shekarar 2013 da aka mika biliyan 120. Ya ce wannan ya faru ne sakamakon faduwar darajar Naira da man fetur, wanda shi ne aka fi dogaro da shi a kasar nan na kudin shiga.