Gwamnatin Jihar Sakkwato ta raba injunan ban ruwa 1000 ga manoma

Gwamnatin Jihar Sakkwato a karkashin jagorancin Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ta raba injunan ban ruwa 1000 ga manoman jihar domin inganta noman rani a jihar.A wurin bikin raba injunan wanda aka gudanar a makon jiya a garin Kasarawa Gwamnan Jihar Ribas Mista Rotimi Amaechi, wanda ya jagoranci raba injunan a gaban Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad […]

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta raba injunan ban ruwa 1000 ga manoma
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta raba injunan ban ruwa 1000 ga manoma

Gwamnatin Jihar Sakkwato a karkashin jagorancin Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ta raba injunan ban ruwa 1000 ga manoman jihar domin inganta noman rani a jihar.
A wurin bikin raba injunan wanda aka gudanar a makon jiya a garin Kasarawa Gwamnan Jihar Ribas Mista Rotimi Amaechi, wanda ya jagoranci raba injunan a gaban Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya jinjina wa gwamnatin Sakkwato kan kokarin da take yi don ganin ta inganta sha’anin noma. “Fanin noma da gwamnati ke kokarin habakawa abu ne mai kyau kuma zai kawo dogaro da kai, in har aka samu haka duk wasu matsaloli na tsaro, za a ga sun gushe domin duk al’ummar da ta himmatu ga sana’a da abubwan dogaro da kai, to ba ta da wani lokaci da za ta bata balle ta shiga aikata laifuffukan da za su kawo tashin hankali a kasa,” inji Ameachi.
A jawabin Gwamna Magatakarda Wamakko, ya ce sanin muhimmancin noma ga al’ummar da Allah Ya ba shi jagoranci ya sa yake son bunkasa harkar noma ta hanyar zamani domin a kara inganta samar da abinci.
Ya ce: “Wadannan injuna da muka raba a yau aikin da suke yi a kankanen lokaci mutum 20 za su kwashe yini kafin aiwatar da shi, ka ga ke nan lokaci ya zo an samu ci gaba da rage wahalar noma wadda aka gada kaka da kakanni. Dole a samu canjin lokacin fito da kayan aiki da za su saukake wa manoma wahalar noma.”
Gwamnan ya kuma ce sun sayo wasu injiunan noma domin rabawa ga manoma saboda ba kowane manomi ke iya sayen motar noma ba, kuma wadannan kananan injuna da aka samo, mutum na iya sayensa ko wasu su hadu su saya a kungiyance domin taimaka wa kansu su yi noma mai albarka.
Ya ce dalilinsu na kokarin sauwaka wa manoma shi ne in jama’a suna da ayyukan yi da suke samun kudin shiga, zaman lafiya zai samu, saboda in akwai yunwa zaman lafiya zai yi wuya.

An fara sana’ar hayar Fawa-bank a Kano

’Yan sanda sun kama fasinja ya ɓoye bindiga a cikin burodi 

An kama fasto kan kashe ’yar shekara 13 da duka

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya