Gwamnatin Jihar Yobe za ta tallafa wa wadanda rikicin bara ya rutsa da su

Gwamnatin Jihar Yobe ta ware Naira miliyan 187 don tallafa wa wadanda suka rasa rayukansu da gidajensu da sauran abubuwa a yayin  rikicin da aka yi fama da shi bara. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin kwamishinan ma’aikatar harkokin cikin gida da watsa labarai, Alhaji Boni Fika a jawabinsa ga manema labarai jim kadan […]

Gwamnatin Jihar Yobe za ta tallafa wa wadanda rikicin bara ya rutsa da su
Gwamnatin Jihar Yobe za ta tallafa wa wadanda rikicin bara ya rutsa da su

Gwamnatin Jihar Yobe ta ware Naira miliyan 187 don tallafa wa wadanda suka rasa rayukansu da gidajensu da sauran abubuwa a yayin  rikicin da aka yi fama da shi bara. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin kwamishinan ma’aikatar harkokin cikin gida da watsa labarai, Alhaji Boni Fika a jawabinsa ga manema labarai jim kadan da kammala zaman majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Damaturu.
Kwamishinan ya ce kudin sun kunshi na mutanen da aka kona musu gidajensu da kuma magadan da ’yan uwansu suka rasu a sanadiyyar rikicin ’yan bindiga a sassan da suka yi fama da hakan a fadin jihar.
Kwamishina Fika ya ce tuni hukumar kula da kai daukin gaggawa ta Jahar (SERA) ta kammala lissafta mutanen da lamarin ya shafa  tare da kiyasin asarorin da suka yi. Hukumar ta kiyasta kimanin mutum 99 ne suka rasu da mutum kimanin 135 da aka kona gidajensu da dukiyoyinsu.  An kiyasta asarar dukiya ta kusan Naira miliyan 372, saboda haka za a bayar da tallafin ne don rage radadin abin da ya shafe su.
Hukumar ta SERA  ta nada kwamitin da zai kula da rarraba tallafin ga wadanda abin ya shafa, a karkashin jagorancin shugabanta, Alhaji S. Fawa da sakatarensa, wanda shi ne kwamishinan ma’aikatar watsa labaran, Alhaji Goni Fika.