Gwamnatin Kaduna ta ɗebi ’yan sa-kai 7,000 aiki don magance matsalar tsaro

Gwamnan ya sha alwashin hana ’yan bindiga sakat a fadin Jihar

Gwamnatin Kaduna ta ɗebi ’yan sa-kai 7,000 aiki don magance matsalar tsaro

Gwamnatin Kaduna ta ɗebi matasa 7,000 aikin sa-kai domin ba su horo da nufin magance matsalar tsaron da ta addabi Jihar.

A cewar Gwamnan Jihar, Uba Sani, sun yanke shawarar ɗaukar matasan ne da nufin ƙara su a cikin rundunar Jihar ta ’yan sa-kai (KASVS), domin su hana ’yan bindiga sakat.

Da yake jawabi yayin kaddamar da bayar da horo ga matasan a Kwalejin ’Yan Sanda da ke Kaduna ranar Asabar, Gwamnan ya ce an debo su ne daga dukkan Kananan Hukumomin Jihar domin cika alkawarin da ya yi.

Ya ce, “Daga cikin muhimman manufofinmu, akwai batun ƙara yawan dakarun rundunar ’yan sa-kai (KADVS). Tun bayan kafa ta take ta fadi tashin ganin ta yi aiki da sauran rundunonin tsaro domin dakile bata-gari.

“Amma muna fama da matsalar karancin ma’aikata. Dalili ke nan da gwamnatinmu ta yanke shawarar kara daukar wadannan mutanen.

“Sai da muka yi zuzzurfan bincike sannan muka hada gwiwa da Shugabannin Kananan Hukumomi da kuma masu rike da sarautun gargajiya kafin mu zakulo wadannan zaƙaƙuran matasan,” in ji Gwamnan.

Sai dai ya ja hankulansu da su yi aiki bisa doron doka sannan su guji take hakkin bil Adama yayin gudanar da ayyukansu.

A wani labarin kuma, Gwamnan ya sha alwashin jami’an tsaro za su gano tare da kama wadanda suka kai hari kan masallata a kauyen Saya-Saya na Karamar Hukumar Ikara da ke Jihar ranar Juma’a, inda suka kashe mutane da dama.

Kotu ta kori karar neman hana dalibai sanya hijabi

’Yan kwangila ne dalilin ɗauke wutar lantarki —EFCC

DAGA LARABA: Yadda Almajiri Ya Zama Mabaraci

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya