Gwamnatin Kaduna ta ba zakarun Musabaka kujerun Hajji

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ba gwarzo da gwarzuwar shekara a gasar musabakar kur’ani ta jihar da aka kammala a makon jiya kujerun aikin Hajji. Gwarzon shekarar shi ne Sulaiman Saleh daga karamar Hukumar Ikara ita kuma gwarzuwar shekara ita ce Wasila Haliru daga karamar Hukumar Sabon Gari, kuma dukkansu za su wakilci jihar a gasar […]

Gwamnatin Kaduna ta ba zakarun Musabaka kujerun Hajji
Gwamnatin Kaduna ta ba zakarun Musabaka kujerun Hajji

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ba gwarzo da gwarzuwar shekara a gasar musabakar kur’ani ta jihar da aka kammala a makon jiya kujerun aikin Hajji. Gwarzon shekarar shi ne Sulaiman Saleh daga karamar Hukumar Ikara ita kuma gwarzuwar shekara ita ce Wasila Haliru daga karamar Hukumar Sabon Gari, kuma dukkansu za su wakilci jihar a gasar kasa da za a yi a Jihar Jigawa a watan gobe. Da yake jawabi a wurin rufe gasar, Gwamnan Jihar Mukhtar Ramalan Yero ya ba alkalai maza biyu da mata biyu da suka yi alkalancin gasar kujerun Hajji, kuma ya ba kwamitin shirya musabakar kujera daya.  Gwamna Yero ya kuma ba sauran ’yan takarar kyautar kudade da suka kama daga Naira dubu 10 zuwa dubu 50. Ya ce ya ba wadanda suka shiga gasar amma ba su nasara ba kyauta ne domin duk mahaddacin kur’ani abin girmamawa ne. Daga nan sai ya nemi Musulmi su kauce wa hassada ya kuma shawarce su da su rika tsoron Allah a duk abin da suke yi.  A jawabinsa, shugaban kwamitin Masabaka na jihar, Dokta Abdulkadir Bello Salanke Zazzau yaba wa Gwamnan ya yi a kan taimakon da yake ba su domin ci gaban addinin Musulunci.