Gwamnatin Kaduna ta haramta zanga-zanga a jihar

Gwamnatin ta ɗauki matakin ne biyo bayan tarzoma da aka samu yayin zanga-zangar yunwa a jihar.

Gwamnatin Kaduna ta haramta zanga-zanga a jihar

Gwamnatin Jihar Kaduna, ta haramta duk wani taro ko zanga-zanga, yayin da zanga-zangar #EndBadGovernance ta ƙare a ranar Asabar.

Majalisar Tsaron Jihar, ta bayyana cewa ta yanke wannan shawarar ne domin hana ɓata gari fakewa da zanga-zanga wajen aikata laifi a jihar.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan ya fitar a ranar Asabar.

Aruwan, ya bayyana cewa duk da cewa gwamnatin jihar na girmama haƙƙin ‘yan ƙasa na faɗar albarkacin baki da gudanar da taro cikin lumana, amma ba za ta amince da aikata laifuka ba.

Ya bayyana cewa cewa duk wani taro zanga-zangar da jami’an tsaro ba su aminta da shi ba, haramtacce ne a jihar.

Aruwan, ya kuma bayyana cewa abubuwan da suka faru yayin zanga-zangar yunwa a jihar, ya nuna yadda wasu ke fakewa don cutar da waɗanda ba su ji ba su gani ba.

Ya ƙara da cewa rahotannin sirri sun nuna yadda ɓata gari suke son cimma mummunan manufarsu da suna zanga-zanga.

Sai dai Aruwan, ya yi gargaɗi cewa duk wanda ya bari ya shiga a sunan tada tarzoma a jihar zai fuskanci hukunci.

Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar da jami’an tsaro ba za su bar kowa ya tada hankali a jama’a ba.

Ya kuma roƙi jama’ar jihar da su mutunta dokar hana fita daga ƙarfe 6 na yamma zuwa ƙarfe 8 na safe da gwamnatin ta sanya.

HOTUNA: Tankar mai ta yi bindiga a Dikko Junction

An kashe manyan alƙalai 2 a harabar Kotun Ƙolin Iran

’Yan Yahoo sun harbe jami’in EFCC har lahira a bakin aikinsa

Farashin kayan abinci ya faɗi warwas a Neja