El-Rufai ya kaddamar da rushe gidaje a Zariya
Mazauna yankin sun koka tare da neman dauki daga gwamnatin jihar.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta kaddamar da rusa dubban gidajen da ke bayan Kwalejin Tukin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAT) da ke Zariya a ranar Litinin.
Rusau din ya biyo bayan kwashe shekaru ana tafka shari’a tsakanin hukumar kwalejin da masu gidajen da take zargi da yin kutse a filin kwalejin.
Wasu daga cikin masu gidaje da Aminiya ta zanta da su kan lamarin sun bayyana cewa suna rokon gwamnati da ta tausaya ta tallafa musu.
Al’ummomin sun yi kira da cewa su ’yan kasa ne ba baki ba kuma sun bi duk dokokin da suka dace kafin su yi gini a filayen nasu da saya suka yi.
Aminiya ta ga yadda mutanen da aka rushe gidajen nasu ke ta kwashe kayayyakinsu da kuma balle wasu daga cikin kayan rufin gidajensu da kansu.
Wannan ba shi ne karo na farko da gwamnatin jihar karkashin jagorancin Nasir El-Rufai ke rushe wuraren da mutane suke zaune ba bisa ka’ida ba a jihar.