Gwamnatin Kaduna ta raba irin masara ga manoma
Gwamnatin Jihar Kaduna ta raba kyautar irin masara kilo dubu biyar ga manoma a yunkurinta na karfafa wa manoma gwiwa a fannin aikin gona. Da yake jawabi lokacin raba irin wanda Kamfanin Balue Seed ya samar, Manajan Shiyya na Hukumar Bunkasa Aikin Gona da ke Maigana a Jihar Kaduna, Alhaji Ahmed Abubakar ya ce irin […]
Gwamnatin Jihar Kaduna ta raba kyautar irin masara kilo dubu biyar ga manoma a yunkurinta na karfafa wa manoma gwiwa a fannin aikin gona.
Da yake jawabi lokacin raba irin wanda Kamfanin Balue Seed ya samar, Manajan Shiyya na Hukumar Bunkasa Aikin Gona da ke Maigana a Jihar Kaduna, Alhaji Ahmed Abubakar ya ce irin wanda Gwamna Nasiru Ahmed El-Rufa’i ya bayar, ya yi haka ne domain manoma su san cewa bai manta da su ba kuma a shirye yake ya bayar da dukkan wata gudunmawa domin ci gaban aikin gona a Jihar Kaduna.
Alhaji Ahmed Abubakar ya ce manoman da suka amfana da wannan karamci su ne wadanda suka samu horo kan noman masara da GIZ da OCP suka horar da su.
A cewarsa ana sa ran za a yi amfani da irin a hekta 250 kuma ana sa ran samun buhu 40 a duk hekta daya.
Manajan ya yi bayanin cewa Shiyyar Maigana ta samu kilo 1,700 wanda zai a yi amfani da shi a hekta 85 kuma ana sa ran za a samu buhun masara 3,400 a karshen daminar bana.
Ya yi amfani da wannan dama inda ya yi kira ga manoman da suka amfana da irin kan su yi amfani da shi yadda ya kamata domin wadata Jihar Kaduna da abinci.