Gwamnatin Kaduna ta raba Keke Napep dubu ga ’yan acaba

A ranar Litinin ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta raba wa kungiyar ’yan acaba Keke Napep dubu daya domin inganta harkokin sufuri a fadin jihar.A watan jiya ne gwamnatin jihar ta hana aiki da babura a kananan hukumomi takwas, a wani shiri na magance rashin tsaro da kuma rage cinkoson ababen hawa a jihar.Wannan mataki na […]

Gwamnatin Kaduna ta raba Keke Napep dubu ga ’yan acaba
Gwamnatin Kaduna ta raba Keke Napep dubu ga ’yan acaba

A ranar Litinin ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta raba wa kungiyar ’yan acaba Keke Napep dubu daya domin inganta harkokin sufuri a fadin jihar.
A watan jiya ne gwamnatin jihar ta hana aiki da babura a kananan hukumomi takwas, a wani shiri na magance rashin tsaro da kuma rage cinkoson ababen hawa a jihar.
Wannan mataki na hana baburan ya janyo kace-nace a tsakanin mazauna jihar, inda jama’a suka koka tare da yin Allah-wadai da matakin gwamnatin.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da baburan a gidan gwamnatin Jihar Kaduna, Gwamna Mukhtar Ramalan Yero ya ba mutanen jihar hakuri, musamman wadanda ba su ji dadin matakin da gwamnatinsa ta dauka na hana sana’ar babur a jihar ba.
“Muna sane da cewa a lokacin da muka dauki matakin hana hawan babur wasu mutane sun ji dadi, wasu kuma ba su ji dadi ba. Muna yi wa wadanda suka ji dadi godiya bisa goyon bayan da suka ba mu. Su kuma wadanda ba su ji dadin hana hawan babur ba muna ba su hakuri.
“Ina so mutane su gane cewa a matsayinmu na shugabannin, dole ne mu fada wa junanmu gaskiya. Babu yadda za mu bar jiharmu ta zama juji, saboda haka dole ne mu gyara jiharmu, don haka nake cewa kada a zargi majalisa a kan hana babur, ni za a zarga kuma na dauki nauyin duk abin da za a ce, saboda ni ne shugaba,” inji shi.
Ya ce ko masu sana’ar babura a kullum suna rokon Allah Ya sama musu wata sana’ar da za ta zama alheri a gare su ne, domin ba a sonsu suke wannan sana’ar acaba ba.
Ya ce gwamnati ta bayar da Keke Napep a kan Naira dubu 500 kowacce, kudin da ya hada da fenti da na rijista da lamba, inda za su rika biya kadan-kadan har shekara daya.
A lokacin da yake jawabin godiya Shugaban masu acaba na Jihar Kaduna Malam Garba Rabi’u ya ce ’yan kungiyarsu murna sakamakon cika alkawari da gwamna ya yi na ba su wadannan babura, sannan ya ce a shirye suke su sake zabarsa a zabe mai zuwa.