Gwamnatin Kaduna ta sassauta dokar hana fita

Gwamna jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya sanar da sassauta dokar hana fita ta sa’a 24 da aka sanya a jihar tun ranar Lahadi sakamakon kalubalen tsaro. Mai taimakawa Gwamnan a harkar watsa labarai Gwamnan, Samuel Aruwan ya ce, Gwamnatin jihar ta dauki wannan matakin ne bayan da aka kammala taron majalisar tsaro ta jihar. An […]

Gwamnatin Kaduna ta sassauta dokar hana fita

Gwamna jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya sanar da sassauta dokar hana fita ta sa’a 24 da aka sanya a jihar tun ranar Lahadi sakamakon kalubalen tsaro.

Mai taimakawa Gwamnan a harkar watsa labarai Gwamnan, Samuel Aruwan ya ce, Gwamnatin jihar ta dauki wannan matakin ne bayan da aka kammala taron majalisar tsaro ta jihar.

An sassauta dokar a Kasuwan Magani da Kujama inda jama’a zasu iya fita daga karfe 6 na safe zuwa karfe 5 na yamma. Yayin da a birnin Kaduna a yanzu dokar za ta fara aiki daga karfe 5 na yamma zuwa karfe 1 na rana. Hakan na nufin mutane za su iya zirga-zirgarsu da harkokinsu a birnin tsakanin karfe 1 na rana zuwa karfe 5 na yamma.