Gwamnatin Kaduna za ta binciki gobarar Fanteka
Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce za ta gudanar da bincike domin gano musabbabin gobara da ta cinyeý sashen ’yan Katako da ke a kasuwar Panteka a Tudun Wada, Kaduna. ’Yan kasuwar sun yi hasarar miliyoyin Nairori a sakamakon gobarar, wadda ta cinye shaguna masu yawan gaske. Wutar ta auku ne da misalin karfe 2 na […]

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce za ta gudanar da bincike domin gano musabbabin gobara da ta cinyeý sashen ’yan Katako da ke a kasuwar Panteka a Tudun Wada, Kaduna.
’Yan kasuwar sun yi hasarar miliyoyin Nairori a sakamakon gobarar, wadda ta cinye shaguna masu yawan gaske. Wutar ta auku ne da misalin karfe 2 na daren ranar Juma’ar da ta gabataý kuma har yanzu babu wanda ya san sanadiyarta.
Gwamnan jihar, Malam Nasir El-rufai wanda ya ziyarci kasuwar, ya jajanta wa ’yan kasuwar, musamman ýwadanda suka rasa shagunansu. Ya ziyarci wajen ne tare da tawagar wasu manyan jami’an gwamnati, inda ya bai wa ’yan kasuwar tabbacin yin bincike domin gano musabbabin gobarar.
“A matsayinmu na shugabanni, za mu tabbatar da mun gano musabbabin wannan gobara domin magance sake aukuwar lamarin nan gaba. Allah Ya mayar maku da mafificin alherin abin da kuka rasa,” inji shi.
Aminiya ta gano cewa akalla runfuna saba’in ne suka kone a kasuwar. Aminiya ta ziyarci kasuwar, inda ta tarar da ’yan kasuwa na jimamin abin da ya faru, yayin da wasu ke tattara sauran komatson da ba su kone ba. Wasu kuma suna ta kuka tare da yin kururuwa saboda hasarar da suka yi.
Aminiya ta fahinci cewa gobarar ta faro ne daga sashen ’yan katako kafin ta bazama zuwa sauran sassan kasuwar. Yakubu Ibrahim, daya ne daga cikin makwabtan kasuwar, ya ce: “Mun ji kara ne kamar abu ya fashe, da muka ruga sai muka ga gobara ce ta faro daga sashen ’yan katako. Kafin masu kashe gobara na gwamnati su zo, gobarar ta riga ta bazu cikin kasuwar,” inji shi.
Kodayake akwai wadanda kuma suke dora alhakin haka ga wutar lantarki. Aminiya ta jiyo cewa wasu daga cikin matasa da suka taro a daren domin kashe gobarar sun hana jami’an kashe gobara da suka zo domin taimakawa saboda wai a cewarsa sun makara.
“Wannan dabi’a ya kamata mutane, musamman matasa su daina ta domin ba za ta taimaka mana ba. A ce duk lokacin da ake gobara idan jami’an kashe gobara sun zo sai matasa su rika jifansu saboda wai sun makara.
“ýWannan ba dabi’a mai kyau ba ce kuma da wuya ka ji irin hakan na faruwa a wasu wurare sai a nan Kaduna kuma a unguwar talakawa. Saboda haka dole mu canza hali,” inji wani dattijo a kasuwar, da bai ambaci sunansa ba.
Daga bisani sai da aka kira ’yan sanda da sauran jami’an tsaro kafin masu kashe gobarar suka samu damar yin aikinsu da safe, bayan wutar ta yi barna. Shi ma Sakataren kungiyar ’Yan kasuwar, Ibrahim Abubakar wanda ya nuna cewa hakika an yi mummunar asara a sakamakon wannan gobara, ya tabbatar da cewa runfuna sama da saba’in ne suka kone.