Gwamnatin Kaduna zata fara biyan ma’aikata sabon albashi

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da fara biyan sabon karancin albashi na Naira dubu 30 daga ranar 1 ga watan Satumba 2019, kamar yadda mai taimakawa Gwamnan jihar Kaduna na musamman akan watsa labarai Muyiwa Adekeye ya sanar a yau Litinin. An dai sanar da hakan ne yayin zaman majalisar zartarwar jahar daya gudana a […]

Gwamnatin Kaduna zata fara biyan ma’aikata sabon albashi

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da fara biyan sabon karancin albashi na Naira dubu 30 daga ranar 1 ga watan Satumba 2019, kamar yadda mai taimakawa Gwamnan jihar Kaduna na musamman akan watsa labarai Muyiwa Adekeye ya sanar a yau Litinin.

An dai sanar da hakan ne yayin zaman majalisar zartarwar jahar daya gudana a yau Litinin wanda Mataimakiyar Gwamnan Kaduna Dakta Hadiza Balarabe, ta jagoranta. Gwamnatin Kaduna ta dauki wannan mataki ne domin inganta walwalar ma’aikatan jahar.

Fara aiwatar da biyan sabon karancin albashi na kasa na Naira dubu 30 zai kara adadin kudaden da gwamnatin jahar Kaduna ke kashewa wajen biyan albashi da kashi 33 cikin 100, wato daga Naira biliyan 2.827 zuwa Naira biliyan 3.759, wannan karin kudin ya kai na kusan Naira biliyan 1 wanda albashi da fansho zai kwashi kaso mai tsoka na kudaden jihar Kaduna.