Gwamnatin Kamaru ta daura yaki da ledoji don kare muhalli

Hukumomin a Kamaru sun daura yaki da ledoji, don haka suka tunatar da manyan ‘yan kasuwa da kuma sauran jama’a cewa ya rage wa’adin watanni bakwai nan gaba da su tsaida sarrafa ledoji, sanfurin wadanda ba sa narkewa a cikin kasa.  Ko kuma a daina amfani da su kwata-kwata. Don irin wadannan ledojin na gurbata […]

Gwamnatin Kamaru ta daura yaki da ledoji don kare muhalli

Ledoji da ke gurbata muhalli a kasar KamaruHukumomin a Kamaru sun daura yaki da ledoji, don haka suka tunatar da manyan ‘yan kasuwa da kuma sauran jama’a cewa ya rage wa’adin watanni bakwai nan gaba da su tsaida sarrafa ledoji, sanfurin wadanda ba sa narkewa a cikin kasa.  Ko kuma a daina amfani da su kwata-kwata. Don irin wadannan ledojin na gurbata muhalli da illata kasa. Lamarin da ke hana tsiro toho. Wannan al’amari na haifar da matsala wajen sake sarrafa shara ga kamfanin HYSACAM, wand ake da nauyin kwashe shara.
Bincike ya nuna cewa daga cikin ton din shara 700 da kamfanin  ke tattarawa a kowacce wayewar gari a manyan biranen kasa, 14 daga ciki duk na kayan ledojin da ba a iya sarrafasu ne.
 Ministan kare muhalli ya ce daga watan Maris na shekara mai zuwa ne dokar haramta yin amfani da ledoji marasa narkewa a cikin kasa za ta fara aiki akan kamfanonin da suke kerasu da kuma kananan ‘yan kasuwan da suke sayarwa.  A cewar mataimakin daraktan kula da kayan bola da kuma sinadaran kimiyya masu kunshe da guba a ma’aikatar kula da kare muhalli:
“Wadannan ledojin na toshe magudanun ruwa, wanda kuma shi ne daya da cikin dalilan da ke haddasa ambaliya. Sa’anna kuma a duk sa’adda ledojin suka nutse a cikin kasa suna zamewa wani matarin  da ke hana ruwa ratsa cikin kasa. Kuma yana haifar da karancin samun albarkatun noma. Game da batun da ya danganci kiwon lafiya, bakin hayakin da yake tasowa daga kona wadannan ledojin da ake yi a sarari na kunshe da wasu abubuwa masu hadassa illa ga kafofin shakar numfashi, tunda ana sarrafa su ne daga tukar man fetur. Don haka ma bai kamata da a rika nade tuwo da wadannan ledojin ba.” Inji shi.
Wani kuwa ya shaida wa wakilimu cewa “Ni kam ban san abin da zan ce ba, idan gwamnati ta hana sayar da wadannan ledoji, ni kam na bari ba, idan kuma ba haka ba sai na ci gaba da kasuwancin. Ina da yara da iyali, ga shi kuma a cikin kasuwancin nake biyan haya da karatun yara. Ni dai ba ni da wata dabara da zan yi kuma. Na san dai kawai ledojin na amfana wa jama’a da dama”.Wannan kuma akasin haka ya gani: “Babu ta yadda zan fasa wannan kasuwancin saida ledoji an haifeni a ciki, na girma a ciki. Hukuma ba ta tuntubemu ba, domin ba mu wani bayani face kawai zartawar da take yi da kamfanonin da suke kera ledojin”.Sai dai akwai bayani daga bangaren gwamnati na cewa za a fara kera ledojin da za a iya sake sarrafasu, domin rage gurbacewar muhalli. Wanda har idan aka kai watan Maris ’yan a ci gaba da amfani da irin ledojin da aka haramta za a ci shi tara daga Miliyan 5na CFA izuwa miliyan 10 tare da zaman gidan yari  na tsawon shekaru biyu zuwa 10.