Gwamnatin Kamaru ta rufe sama da coci 50

Gwamnatin kasar Kamaru ta rufe majami’u sama da 50 a yunkurinta na rufe majami’u kusan 100 na cocin Pentecostal a wannan wata.Shugaba Paul Biya na Kamaru ya ce, rufe majami’un wani yunkuri ne na dakile fastocin Pentecostal daga aiwatar da “miyagun ayyuka” da ake zargin suna barazana ga zaman lafiyar Kamaru. Kuma zuwa yanzu jami’an […]

Gwamnatin Kamaru ta rufe sama da coci 50
Gwamnatin Kamaru ta rufe sama da coci 50

Gwamnatin kasar Kamaru ta rufe majami’u sama da 50 a yunkurinta na rufe majami’u kusan 100 na cocin Pentecostal a wannan wata.
Shugaba Paul Biya na Kamaru ya ce, rufe majami’un wani yunkuri ne na dakile fastocin Pentecostal daga aiwatar da “miyagun ayyuka” da ake zargin suna barazana ga zaman lafiyar Kamaru. Kuma zuwa yanzu jami’an gwamnati sun rufe akalla majami’u 50, kuma za a rufe sauran a nan gaba.
Jami’an gwamnatin Kamaru sun ce majami’un Pentecostal sun zama cuta ga zaman lafiyar kasar, saboda jabun mu’ujizar warkar da marasa lafiya da sauran jabun mu’ujizoji da suke yi. Gwamnatin ta kawo misali da mutuwar wata yarinya ’yar shekara tara a wurin wata addu’a a ranar Lahadin da ta gabata, yayin da wani faston Pentecostal ya yi yunkurin cire mata aljanu daga jikinta.
Wani jami’in gwamnatin Kamaru Mbu Anthony Lang, ya shaida wa gidan talabijin na CNN cewa majami’u 50 ne kacal daga cikin majami’un Pentecostal 500 da ke kasar doka ta san da su.
 “Za mu yi waje da wadannan masu kiran kansu fastocin Pentecostal da suke bata sunan Isa Almasihu ta wajen jabun mu’ujizoji suna kashe jama’a a majami’unsu,” inji Mba Lang, wanda ya ce, “Sun rusa damar da suke da ita.”
Kashi 54 na al’ummar Kamaru miliyan 20 mabiya addinin Kirista ne, kuma mutum dubu 800 daga cikinsu suna bin cocin Pentecostal ne wadanda suke karuwa da kashi bakwai a kowace shekara.
Kamaru wadda ke bin akidar sekulanci, tsarin mulkinta ya amince da ’yancin zabin addini ga jama’arta ciki har da na sauya addini.
Bishop Boniface Tum, na majami’ar Cameroonian Church of God, ya shaida wa CNN cewa harin da gwamnati ke kai wa majami’un Kiristocin kasar keta hakkin dan Adam ne. “Amincewar hukuma da cocin Katolika da na Presbysterian da Baptist da kuma Musulunci da sauran wasu coci-coci wani mugun tauye hakkin addini ne,” inj Tum.
Wani Fasto mai suna Fasto Elie Pierre wanda aka rufe cocinsa a makon jiya ya rika karfafa gwiwar masu zuwa cocin ta lasifika cikin babbar murya cewa, “Muna da ’yancin kare kanmu.”
Wasu jama’a sun nuna gamsuwa da rufe majami’un inda wani mai sharhi ya bayyana hakan da “Labari mai dadi” kuma ya ce “Ina fata sauran kasashen Afirka za su yi haka. Kun kyauta Kamaru.”