Gwamnatin Kano da kamfanin Pfizer sun gina cibiyar lafiya ta Naira biliyan hudu

Gwamnatin Jihar Kano a karkashin  shugabancin Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso na shirin kaddamar da wata cibiyar lafiya da aka kashe sama da Dalar Amurka miliyan 25 (kimanin Naira biliyan hudu) a karamar Hukumar Dawakin Kudu da ke jihar. Wata majia mai tushe a shaida wa Aminiya cewa cibiyar lafiyar tana da gadaje 100 kamfanin harhada […]

Gwamnatin Kano da kamfanin Pfizer sun gina cibiyar lafiya ta Naira biliyan hudu

Gwamnatin Jihar Kano a karkashin  shugabancin Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso na shirin kaddamar da wata cibiyar lafiya da aka kashe sama da Dalar Amurka miliyan 25 (kimanin Naira biliyan hudu) a karamar Hukumar Dawakin Kudu da ke jihar.
Wata majia mai tushe a shaida wa Aminiya cewa cibiyar lafiyar tana da gadaje 100 kamfanin harhada magunguna na Pfizer ne ya gina ta da hadin gwiwar gwamnatin Jihar Kano, kuma an tsara zai rika binciken cututtuka masu saurin yaduwa da yadda za a magance su.
Cututtukan da cibiyar za ta mayar da hankali wajen bincike da magance su, sun hada da cutar amai da gudawa da shan inna da kanjamau da sauransu.
Majiyyarmu ta ce an tsara cibiyar za ta zama babbar cibiyar horar da likitoci da malaman kiwon lafiya a jihar da makwabtanta. Haka kuma cibiyar za ta rika tallafa wa wajen kai agajin gaugawa yayin da aka samu barkewar cututtuka don magance su cikin hanzari.
Kamfanin Pfizer wanda shi ne ya ba da gudunmawar kayan aikin, ya ce cibiyar za ta kasance daya daga cikin cibiyoyin kula da lafiya da ke jihar. Kuma ana sa ran cibiyar za ta samar da guraben ayyuka ga jama’a.
Tuni gwamnatin Jihar Kano ta fadada da gyara hanyoyin da ke hade kauyukan yankin da cibiyar tare da sanya fitilun hanya a cibiyar.
Mista Dabid Odiwor Babban Sakataren Cibiyar Lafiya da Magance Cututtuka mai zaman kanta, wanda shi ne ya kula da yadda aka gudanar da ginin cibiyar ya ce gini da kuma kayan aikin da aka samar a cibiyar masu inganci ne. Ya ce makamanciyar wannan cibiya da a yanzu aka gina a kasar Uganda ba ta kai ta Kano ba.
Ya ce cibiyar ta Uganda ana gudanar da ita ce ta hanyar hadakar cinikayya mai dogaro da kai, wanda hakan ke ba cibiyar damar samun tallafin kungiyoyi da hukumomi a duniya, don haka ana sa ran wadda aka gina a Kano ma za ta bi sahu da zarar an bude ta.
An kafa kwamitin mutum shida da zai ke kula da asusun gudanarwar cibiyar a karkashin shugabancin Farfesa Shehu Galadanci. Sauran mambobin kwamitin sun hada da Ibrahim A. Haruna da Adamu Jafiya da Adamu Aliyu Kiyawa da Habib Sadauki da Farfesa Auwalu Yadudu.