Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki
An tanadi cibiyoyi 91 domin raba wa mabuƙata 91,000 abincin buɗa-baki duk rana nan da tsawon kwanaki 27 masu zuwa.

Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki domin tallafa wa mabuƙata a wannan wata mai albarka na Ramadana.
Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya ƙaddamar da rabon abincin a cibiyar Dandali da ke Ƙaramar Hukumar Fagge a jihar.
- HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja
- NLC ta yi fatali da yunƙurin ƙara kuɗin lantarki
Bayanai sun ce gwamnatin jam’iyyar NNPP ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ta ƙaddamar da wannan shiri tana da burin raba abincin buɗa-baki ga mabuƙata masu azumtar watan Ramadana.
Gwamnatin ta ce an tanadi cibiyoyi 91 domin raba wa mabuƙata 91,000 abincin buɗa-baki duk rana nan da tsawon kwanaki 27 masu zuwa.
Domin tabbatar da samun nasara, gwamnatin ta ce ta ɗauki masu aikin girke-girke da za su riƙa dafawa sannan su raba wa mabuƙata abincin.
Mataimakin Gwamnan wanda shi ne ke jagorantar shirin raba abincin a bana, ya bayyana gamsuwarsa da yadda aka ƙaddamar da shirin, yana mai kiran waɗanda aka ɗora wa alhakin aikin su tabbatar da raba wa mabuƙata abincin a kan kari.
Aminiya ta ruwaito cewa, Mataimakin Gwamnan ya samu rakiyar wasu ƙusoshin Gwamnatin Kano wajen ƙaddamar da rabon abincin da suka haɗa da Kwamishinan Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya da Kwamishinan Harkokin Addini, Sheikh Tijjani Auwal da sauransu.
Gwamnatin Kano ta jaddada ƙudirinta na rage raɗaɗin al’umma musamman Musulmi a wannan wata mai falala.