Gwamnatin Kano ta ƙaryata rahoton barkewar cutar ƙyanda

An ruwaito samun bullar cutar ƙyanda a unguwar Sharada, Madatai, da kuma Gandun Albasa.

Gwamnatin Kano ta ƙaryata rahoton barkewar cutar ƙyanda

Taswirar Kano

Gwamnatin Kano ta yi amai ta lashe dangane da rahoton barkewar cutar kyanda kwanan nan a Karamar Hukumar Birni ta jihar.

A ranar Lahadin da ta gabata ne jami’an lafiya na Karamar Hukumar Birnin suka tabbatar da barkewar cutar a wasu unguwannin karamar hukumar.

Aminiya ta ruwaito cewa, jami’in kula da lafiya a matakin farko na karamar hukumar, Aliyu Jinjiri Kiru, ya bayyana cewa yankunan da aka samu bullar cutar kyanda sun haɗa da Sharada, Madatai, da kuma Gandun Albasa.

Jinjiri ya bayyana cewa an samu rahoton bullar cutar kyanda da sauran cututtuka masu yaduwa ne a cibiyoyin kiwon lafiya da dama a karamar hukumar.

Jami’ar yada labaran yankin, Fatima Abdullahi ta kuma ruwaito shi yana kira da a dauki matakin gaggawa na shawo kan cutar da kuma hana yaduwarta.

Sai dai a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai karkashin ma’aikatar lafiya ta jihar mai ɗauke da sa hannun Daraktan kula da cututtuka masu yaduwa, Dokta Imam Wada Bello ta ce labarin barkewar cutar karya ce zalla.

Dokta Imam ya ce kafin a ayyana cuta a matsayin annoba, akwai wasu matakai da ake bi, kuma jami’an lafiyar karamar hukumar ba su bi wadannan ka’idoji ba, kawai suka yi riga malam masallaci wajen ayyana barkewar cutar.

Darakta Imam ya ce ma’aikatar harkokin lafiya ta jihar Kano na iya bakin kokarin ta wajen sanya idanu kan cututtuka masu yaduwa da kuma hana su barkewa don haka ba hakki ne na jami’an lafiya matakin karamar hukuma su sanar da barkewar cuta ba, hakki ne na ma’aikatar lafiya a mataki na jiha.

Daga nan kuma ya buƙaci al’ummar jihar su kwantar da hankalin su, babu annobar cutar a dukannin fadin kananan hukumomi 44 na jihar ta Kano.

Zaɓen Edo: Yadda aka kama masu sayen ƙuri’a da ’yan daba

Sarakunan Nijar sun kai wa Gwamnatin Yobe ziyarar jaje

Ɗan majalisa ya yi jinjina kan naɗa Danyaya Sarkin Ningi

’Yan Sanda sun kama gungun ’yan fashi 7 a Katsina