Gwamnatin Kano ta ayyana dokar ta-ɓaci a fannin ilimi

Kwamishinan Ilimi na Kano, ya bayyana rashin isassun malamai da kayan koyarwa a matsayin manyan kalubalen da ilimi ke fuskanta a Kano.

Gwamnatin Kano ta ayyana dokar ta-ɓaci a fannin ilimi

A wani yunkuri na kawo gyara a fannin ilimi, gwamnatin Kano ta bayyana shirin aiwatar da dokar ta-ɓaci a fannin a dukkanin kananan hukumomi 44 na jihar.

Kwamishinan Ilimi, Umar Haruna Doguwa ne ya bayyana hakan a yayin taron horar da sabbin sakatarorin ilimi na kwana biyu a Dutse, jihar Jigawa, a ranar Litinin 29 ga Afrilu, 2024.

Doguwa ya bukaci sakatarorin ilimin da su bi dokokin ilimi na jihar, tare da jaddada matsayinsu na wakilan gwamnati a yankunan da aka ba su.

Ya kuma yi gargaɗin a guji sauya wurin aikin malamai zuwa babban birnin jihar saboda wasu dalilai na kashin kai, yana mai jaddada cewa dole ne a kawo karshen wannan ɗabi’a.

Kwamishinan ya bayyana rashin isassun malamai da kayan koyarwa a matsayin manyan kalubalen da ilimi ke fuskanta a Kano.

Sai dai ya bayar da tabbacin cewa gwamnati ta himmatu wajen sake fasalin fannin domin magance waɗannan matsaloli.

Ana sa ran sabbin sakatarorin ilimi da aka naɗa, za su yi aiki tukuru domin ganin an samu ingantaccen ilimi a faɗin jihar.

Shugaban Hukumar Kula da Ilimin Bai Ɗaya ta jihar Kano (SUBEB) Yusuf Kabir ya yaba wa sabbin sakatarorin ilimi bisa jajircewarsu na tunkarar kalubalen ilimi.

Ya bayyana bukatar magance matsalolin da suka haɗa da: karancin saka yara a makarantu, rashin karatu a tsakanin malamai da ɗalibai, da rashin haɗin kai da tallafi daga wajen al’umma.

Kabir ya kuma amince da karancin kwararrun malamai da kuma rashin jajircewa daga ma’aikatan da ba malamai ba a hedikwatar Hukumar Ilimi ta Karamar Hukumar (LEA).

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume