Gwamnatin Kano ta ayyana hutun sabuwar Shekarar Musulunci

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da ayyana hutun ne la’akari da muhimmancin kalandar Musulunci.

Gwamnatin Kano ta ayyana hutun sabuwar Shekarar Musulunci

Gwamnatin Kano ta ayyana gobe Talata, 16 ga watan Yunin 2026, a matsayin hutun rana ɗaya na sabuwar shekarar musulunci ta 1448 Hijiriyya.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Ofishin Shugaban Ma’aikatan Kano ya fitar a yammacin wannan Litinin ɗin.

Sanarwar wadda Darektar Harkokin Gudanarwa da Mulki a Ofishin Shugaban Ma’aikatan, Safiyya Ali Suleiman ta fitar, ta buƙaci ma’aikatan jihar da su yi amfani da wannan dama domin yi wa jihar da kuma ƙasa baki ɗaya addu’ar zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa.

Safiyya ta ce dukkan ofisoshin gwamnati da cibiyoyin gwamnati za su kasance a rufe a ranar Talata domin bai wa ma’aikata da mazauna jihar damar gudanar da bukukuwan sabuwar shekarar Musulunci.

Sanarwar ta bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da ayyana hutun ne la’akari da muhimmancin kalandar Musulunci da kuma al’adar da Jihar Kano ta daɗe tana yi na girmama farkon sabuwar shekarar Musulunci.

Aminiya ta ruwaito Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, a jiya Lahadi yana ba da umarnin fara duban jinjirin watan Muharram na sabuwar shekarar musulunci ta 1448 daga yau Litinin, 29 ga watan Zhul Hijjan 1447.

Kawo yanzu Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Islama da Sarkin Musulmin ke jagoranta ba ta sanar da ganin jinjirin watan na Muharram ba.