Gwamnatin Kano ta ayyana Litinin hutun Ranar Takutaha
Mutanen Kano sun shafe shekaru aru-aru suna gudanar da bikin Ranar Takutaha.
Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana ranar Litinin mai zuwa wadda za ta yi daidai da 23 ga watan Satumba, a matsayin ranar hutun Takutaha.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar da Sakataren Ofishin Shugaban Ma’aikatan Jihar, Abba Danguguwa, ya sanya wa hannu da cewa hutun yana cikin girmama ranar bakwai ga haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W).
- Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron MDD
- An haramta wa ma’aikatan Asibitin Tarayya yin ‘kirifto’ a wurin aiki
“Mutanen Kano sun shafe suna bikin wannan rana a matsayin Ranar Takutaha.
“Bikin Ranar Takutaha wani tsohon tarihi ne da aka shafe shekaru aru-aru ana gudanarwa”
Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar da su yi amfani da lokacin domin yin tunani a kan koyarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da sanya su cikin harkokinsu na yau da kullum.
Ya kuma bukaci jama’a da su riƙa yin addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaba a Kano da Nijeriya baki ɗaya.
Ya yi addu’ar Allah Ya shiga al’amuranmu a wannan lokaci mawuyaci, Ya kuma ba mu albarkacin wannan damuna.
Idan ba a manta ba, Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin da ta gabata a matsayin ranar Maulidi, domin bai wa Musulmi damar murnar zagayowar ranar haihuwar Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (S.A.W).