Gwamnatin Kano ta ba da Naira miliyan 80 ga wadanda hare-haren Boko Haram ya shafa

Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ya raba ceki na fiye da Naira miliyan 80 a matsayin tallafi ga wadanda hare-haren bam suka shafa a Babban Masallacin Kano da Kasuwar Kantin Kwari da kuma gidan mai na Unguwar Hotoro.A ranar Lahadin da ta gabata ne Gwamna Abdullahi Ganduje ya raba cekin kudin, inda ya […]

Gwamnatin Kano ta ba da Naira miliyan 80 ga wadanda hare-haren Boko Haram ya shafa
Gwamnatin Kano ta ba da Naira miliyan 80 ga wadanda hare-haren Boko Haram ya shafa

Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ya raba ceki na fiye da Naira miliyan 80 a matsayin tallafi ga wadanda hare-haren bam suka shafa a Babban Masallacin Kano da Kasuwar Kantin Kwari da kuma gidan mai na Unguwar Hotoro.
A ranar Lahadin da ta gabata ne Gwamna Abdullahi Ganduje ya raba cekin kudin, inda ya ce abin da gwamnati ta bayar wani abu ne na taimakawa kawai domin babu wani abu da za a ba wadanda abin ya shafa da ya fi rayuwarsu. Ya ce an bayar da kudin ne domin tallafawa ga iyalan wadanda suka rasu da kuma wadanda suka samu raunuka.
Wadansu daga cikin mutanen da suka samu tallafin sun shaida wa Aminiya cewa abin da gwamnatin Kano ta yi musu ya nuna cewa tana tausaya wa duk wadanda hadarin ya shafa domin rage radadin da ya same su ko iyalansu.  
A kididdigar da gwamnati ta gudanar an samu jimillar mutum 289 da hadarin ya shafa, inda mutum 139 suka rasu, 150 suka jikkata a hare-haren da aka kai a jihar.