Gwamnatin Kano ta ba wa Kamfanin Triumph shaguna 64 a Kasuwar Canjin Kudi
Gwamnatin Kano ta mallaka wa kamfanin jaridar Triumph shaguna 64 a sabuwar Kasuwar Canjin Kudi ta Zamani da ta gina a harabar kamfanin.
Gwamnatin Jihar Kano ta mallaka wa kamfanin jaridar Triumph mallakinta shaguna 64 a sabuwar Kasuwar Canjin Kudi ta Zamani da ta gina a harabar kamfanin.
Gwamnatin ta ce kimar shaguna 64 da ta ba wa kafanin dab’in na Triumph a sabuwar kasuwar da ke Karamar Hukumar Fagge, ta kai Naira biliyan 1.4.
- Tankar ruwa ta take wasu kananan yara har lahira a Neja
- NAJERIYA A YAU: Tsutsa Ta Sa Kudin Kwandon Tumatir Kaiwa N20,000 A Kano
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa shaguna 64 da aka bai wa kamfanin na Triumph ya kai kashi daya bisa hudu na sabuwar kasuwar.
Manajan-Darakan Triumph, Alhaji Lawan Sabo-Ibrahim, a bayyana cewa da kashi 25% na hannun jarin shagunan da aka ba wa gwamnatin jihar a kasuwar, nan da dan lokaci kamfanin zai fara samar wa gwamnatin kudaden shiga.
Da take mika shagunan, wakiliyar kamfanin Lamash Properties da ya yi aikin ginin, Hajiya Hadiza Abdulkadir, ta ce “A shekarar 2020 ne gwamnatin jihar ta ba su aikin hadin gwiwar gina Sabuwar Kasuwar Canjin Kudi ta Zamani a harabar kamfanin Triumph da ke Fagge.
“Yarjejeniyar ta tanadi mayar matsugunin Triump zuwa Rukunin Gidaje na Amana da ke Kano da kuma ba wa kamfanin shaguna da kimarsu ta kai Naira biliyan 1.4.”
Manajan-Darakan Triumph, Alhaji Lawan Sabo-Ibrahim, ya ce mallakar shagunan a kasuwar canjin za ta farfado da kamfanin dab’in ta hanyar samar masa kudaden sayen sabbin injina da kayan aiki da kuma kudaden shiga ga kansa da kuma gwamnatin jihar.
Ya roki Allah Ya sa hakan ya zama hanyar gwamnati mai barin gado da mai jiran gado za su yi amfani da ita wajen ganin da dorewar kamfanin na Triumph.