Gwamnatin Kano ta dakatar da shugabannin makarantu uku

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da shugabannin makarantun sakandire guda uku saboda sakaci da aikinsu. Makarantun sun haɗa da Sakandiren ƴan mata GGSS Dawanau, Sakandiren Arabiyya GASS Dawanau, da Sakandiren ƴan mata GGSS  Ƙwa duk a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa. Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa ne ya bada umarnin dakatar da su […]

Gwamnatin Kano ta dakatar da shugabannin makarantu uku

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da shugabannin makarantun sakandire guda uku saboda sakaci da aikinsu.

Makarantun sun haɗa da Sakandiren ƴan mata GGSS Dawanau, Sakandiren Arabiyya GASS Dawanau, da Sakandiren ƴan mata GGSS  Ƙwa duk a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa.

Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa ne ya bada umarnin dakatar da su nan take bayan da ya ziyarci makarantun tsakanani 9:00am zuwa 10:00am a ranar Juma’a.

Gobara ta kone shaguna 10 a Kasuwar Rimi da ke Kano

Shari’ar Zaɓen Kano: INEC ba ta da shaida

Umar Doguwa ya ce ya tarar duk shugabannin ba sa nan kuma ya samu rahoton cewa ba sa zuwa aiki duk ranar Juma’a tsawon lokaci.

Sanarwar da Daraktan wayar da kan al’umma na ma’aikatar, Aminu Yassar ya fitar ta ce kwamishinan ya bada umarnin a maye gurbinsu da shugabanni masu ƙwazo nan take.

Umar Doguwa ya kuma bada umarnin a bai wa malamai huɗu a GGSS Ƙwa da biyu a GASS Dawanau takardun tuhuma saboda rashin zuwa aiki.

Sai dai kwamishinan ya bada umarnin karrama shugabar makarantar sakandiren ƴan mata GGSS Harbau dake ƙaramar hukumar Tsanyawa saboda jajircewar da ta ke nunawa bisa aikinta.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda