Gwamnatin Kano ta dakatar da wani fim mai suna Zarmalulu
Fim ɗin mai suna “Zarmalulu” ana zarginsa da rashin ma’ana sannan an yi masa laƙabi da wani suna mai kama da na baɗala.
![Gwamnatin Kano ta dakatar da wani fim mai suna Zarmalulu Gwamnatin Kano ta dakatar da wani fim mai suna Zarmalulu](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2023/12/GAfYgoVXsAAIT4x.jpg)
Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, Abba El-Mustapha. (Hoto: Twitter/@abbaelmustaph1)
Gwamnatin Kano ta dakatar da wani fim da take zargin ya saɓa ka’ida tare da gayyatar dukkannin wanda suka fito a cikinsa domin sauraron ba’asi.
Hukumar tace fina-finai da dab’i ta Kano ce ta dakatar da fim ɗin mai suna Zarmalulu bayan ƙorafin da aka miƙa mata.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar a ranar Asabar, ta ce ana zargin waɗanda suka shirya fim ɗin sun sanya masa suna na baɗala.
“Biyo bayan ƙorafin da Hukumar ta karɓa daga wasu masu kishin Jihar Kano akan wannan fim ɗin, Shugaban Hukumar, Abba El-Mustapha ya bayyana damuwarsa kan lamarin tare da dakatar da fim ɗin.
“Haka kuma, Abba El-Mustapha ya gayyaci dukkannin wanda suka fito a shirin domin jin ba’asi na yin amfani da ita wannan kalma.”
Bayanai sun ce fim ɗin mai suna “Zarmalulu” ana zarginsa da rashin ma’ana sannan an yi masa laƙabi da wani suna mai kama da na baɗala.
Hukumar ta buƙaci duk waɗanda suka yi ruwa da tsaki a fim ɗin da su bayyana a gaban kwamatin bincike da ta kafa.
Hukumar tace fina-finan na da hurumin dakatar da dukkannin wani fim da bata gamsu da yadda aka shirya shi ba tare da ladaftar da duk wani da ta samu da yin abinda bai kamata a cikin kowane fim ba ko kuma a wajen fim ɗin matsawar ɗan Masana’antar Kannywood ne.