Gwamnatin Kano ta dauki manoma 16,000 a shirin tallafin noma

Shirin na da nufin inganta rayuwar manoma mata da nakasassu.

Gwamnatin Kano ta dauki manoma 16,000 a shirin tallafin noma

Manoma

Gwamnatin Jihar Kano ta dauki mutum 16,000 ’yan asalin jihar a domin su ci gajiyar sabbin shirye-shiryen tallafin noma da ta kaddamar.

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce shirin na daga cikin kudurorin gwamantin jihar na bunkasa harkar noma domin samar da ayyukan yi da kuma wadata jihar da abinci.

Da yake kaddamar da shirin a ranar Alhamis, Ganduje ya ce shirye-shiryen noman na da nufin inganta yanayin rayuwar manoma, musamman mata da nakasassu.

Kazalika shirin na da burin ba wa Kanawa kwarin gwiwar rungumar harkar noma da zimmar magance barazanar karancin abincin da Najeriya ke fuskanta.

Ganduje ya ce gwamnatin Kano za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da kungiyoyi da hukumomin kasashen duniya a fannin bunkasa harkar noma a jihar.

An kaddamar da shirye-shiryen noman ne hadin gwiwar hukumomin KNARDA, NG-CARES, APPEALS, SASAKAWA da Shirin Bunkasa Noma da Kiwo ta Jihar Kano (KSADP).