Gwamnatin Kano ta fara shirin yaƙi da matsalar shara
Sabon Kwamishinan ya ce sun shirya kawo ƙarshen shara da ta addabi jihar.
Gwamnatin Jihar Kano, ta ƙaddamar da wani gagarumin shiri don yaƙar matsalar shara da ta addabi sassa daban-daban na jihar.
Shirin, wanda ke gudana tare da haɗin gwiwar ma’aikatun ciniki da sufuri, zai tabbatar da kwashe sharar da ta taru a kasuwanni da unguwanni cikin gaggawa.
A wasu yankuna na jihar, tulin shara da hayaƙin ƙone bola, na barazana ga rayuwar al’umma, lamarin da ya jawo damuwa a tsakanin mazauna wuraren.
Kwamishinan muhalli, Dokta Dahiru Muhammad Hashim, ya bayyana cewa an fara aikin ne daga kasuwanni kuma za a ci gaba da shi har zuwa cikin unguwanni.
“Abubuwa da dama da suka shafi datti da rashin tsafta ba za mu ƙyale su ba domin kare lafiyar al’umma da tsaftar muhalli,” in ji shi.
Har ila yau, ya ce gwamnatin jihar za ta gayyato kamfanoni masu zaman kansu don zuba jari a harkar sarrafa shara, don sauya sharar zuwa wata hanyar samar wa jama’a arziƙi.