Gwamnatin Kano ta fara shirye-shiryen bikon Sheikh Daurawa

Sheikh Daurawa ya ajiye mukaminsa a ranar Juma’a, biyo bayan kalaman gwamnan jihar.

Gwamnatin Kano ta fara shirye-shiryen bikon Sheikh Daurawa

Gwamnatin Jihar Kano, ta fara shirye-shiryen bikon Shugaban Hukumar Hisbah na jihar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da ya yi murabus daga mukaminsa.

Aminiya ta ruwaito yadda gwamnatin jihar ta tura tawagar Majalisar Malamai ta jihar don ganawa da Sheikh Daurawa tare da rokonsa ya dawo kan kujerarsa na shuagabancin Hisbah.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Jibril Falgore da Babban Limamin Masallacin Kasa da ke Abuja, Sheikh Ibrahim Maqari na daga cikin tawagar da gwamnatin ta tura don bikon malamin.

Idan ba a manta ba, Daurawa ya yi murabus daga shugabancin Hisbah, biyo bayan kalaman gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf na sukar yadda hukumar ke gudanar da ayyukanta.

Sai dai ya zuwa yanzu ba a san abin da suka tattauna da kuma matsayar Sheikh Daurawa game da dawowa shugabancin hukumar ba.

Daurawa ya yi murabus ne kasa da sa’o’i 24 bayan kalaman gwamnan wanda ya jawo cece-kuce a tsakanin al’ummar jihar.

Lamarin dai ya shafi farin jinin gwamnan, musamman a shafukan sada zumunta, inda kowa ke tofa albarkacin bakinsa.

Wasu majiyoyi na kusa da gwamnatin ta NNPP, sun bayyana cewar lamarin ya damu gwamnan matuka.

Majiyoyin sun ce gwamnan ya kasa samun halartar sallar Juma’a saboda damuwa kan kalamansa da suka kai ga murabus din Sheikh Daurawa.

“Gwamnan ya damu matuka da abin da ya faru, wanda hakan ya sa ko sallar Juma’a bai fito ba a gidan gwamnati ba, a ofishinsa ya yi sallah,” in ji majiyar.

Mataimakin Kwamandan Hukumar Hisbah na Kano, Dokta Mujahid Aminuddeen tare da wasu jami’an hukumar sun gana da gwamnan a ranar Asabar.

Kokarin jin ta bakin sakataren yada labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ci tura zuwa lokacin hada wannan rahoton.