Gwamnatin Kano ta fitar da 3bn domin gyaran makarantu
Gwamnan ya jaddada aniyarsa na inganta ilimi a jihar.
Gwamnatin Jihar Kano, ta fitar Naira biliyan uku domin gyaran ajujuwa a dukkanin makarantun jihar da ke ƙananan hukumomi 44.
Gwamna Abba Yusuf ne, ya bayyana hakan a ranar Talata, a wani taron masu ruwa da tsaki a gidan gwamnati da ke Kano.
- An kama mace mai kai wa ’yan bindiga kayan abinci
- Yana da kyau a bai wa sarakuna kariya daga gwamnoni —Atiku
Ya ce an fitar da kuɗin ne don samar da yanayi mai kyau tare da inganta harkar koyarwar ɗaliban jihar.
Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ɗauki jami’an tsaro 17,000 waɗanda za su samar da tsaro a makarantun firamare, tare da ɗaukar ma’aikata 400 a kowace ƙaramar hukuma.
“Za a ɗauki jami’an tsaro a yankin da makarantun firamare suke don tabbatar da tsaron ɗalibai,”in ji shi.
Ya ce kowacce ƙaramar hukumar za ta samu Naira miliyan 25 don yin gyare-gyare a makarantu, wanda hukumar kula da ilimin bai ɗaya ta jihar, za ta sanya ido kan yadda aikin zai gudana.
“Wannan na jaddada ƙudurin gwamnati na inganta ababen more rayuwa musamman a ɓangaren ilimi da samar da ingantaccen yanayin koyo ga ɗalibai,” in ji shi.