Gwamnatin Kano ta gurfanar da Kwamishinan Kwankwaso a kotu
Gwamnatin Jihar Kano ta yi karar tsohon Kwamishinan Lafiya na gwamnatin Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da ta gabata, Dokta Abubakar Labaran Yusuf bisa zarginsa da almundahanar Naira miliyan 47. Wannan bayani ya fito daga bakin Shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci ta Jihar Kano, Kwamared Muhyi Magaji Rimingado a lokacin da yake […]

Gwamnatin Jihar Kano ta yi karar tsohon Kwamishinan Lafiya na gwamnatin Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da ta gabata, Dokta Abubakar Labaran Yusuf bisa zarginsa da almundahanar Naira miliyan 47.
Wannan bayani ya fito daga bakin Shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci ta Jihar Kano, Kwamared Muhyi Magaji Rimingado a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai.
Muhyi ya bayyana cewa wadancan kudi da ake zargin tsohon Kwamishinan da yin sama da fadi da su, kudi ne da aka ware don daliban da gwamantin ta dauki nauyin karatunsu a Jami’ar Mansourah da ke kasar Egypt.
Har ila yau, ya bayyana cewa tun a shekarar 2016 hukumarsa ta fara bincike a kan lamarin, inda a yanzu ta yi karar Kwamshinan a kan laifuka guda uku da suka, wadanda suka saba da sashe na 315 da 123(a) na Kundin Shari’ar Finalkod da kuma sashe na 24 (a)(1) na Kundin Shari’ar hukumar yaki da cin hanci ta Jihar Kano.
Aminiya ta kalato cewa ana sa ran shaidu guda biyar za su bayar da shaida a kan badakalar da ake tuhumar tsohon Kwamishinan ya tafka.