Gwamnatin Kano ta haɗa gwiwa da Media Trust kan inganta harkokin yaɗa labarai

Media Trust ya ziyarci Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, a ofishinsa ranar Juma’a.

Gwamnatin Kano ta haɗa gwiwa da Media Trust kan inganta harkokin yaɗa labarai

Gwamnatin Kano da Rukunin Kamfanin Media Trust Group (MTG) masu wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya da Trust TV da Trust Radio, za su haɗa gwiwa kan inganta harkokin yaɗa labarai.

Wannan na zuwa ne a yayin ziyarar da tawagar Kamfanin ƙarƙashin jagorancin Babban Jami’in Gudanarwarsa, Ahmed Shekarau ta kai wa sabon Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, a ofishinsa ranar Juma’a.

Shekarau ya bayyana jin daɗinsa ga Kwamishinan da ya ba su damar ganawa duk da cewa sun miƙa sanarwar ziyarar a ƙurarren lokaci zuwa, lamarin da ya bayyana a matsayin kyakkyawar  dangantakar da ke Kamfanin MTG da Gwamnatin Kano.

“Muna da yaƙinin cewa mu ’yan juna ne saboda ba ma ɗaukar irin wannan alaƙa da wasa ba. Muna da burin ci gaba da buɗe hanyar sadarwa don inganta haɗin gwiwarmu,” inji Shekarau.

Ya ba da shawarar inganta haɗin gwiwa ta hanyar yaɗa rahotanni kai-tsaye kan muhimman ayyukan gwamnati, shirin bidiyo na mako-mako kan ayyukan gwamnatin jihar, da riƙe yarjejeniyar haɗin gwiwa don daidaita ayyukan gwamnati.

Shekarau ya kuma jaddada muhimmancin isar da muradun Kamfanin MTG, inda ya ba da misali da ƙididdigar masu sauraro da kuma jajircewar kamfanin wajen samun inganci duk da ƙalubalen da ake fuskanta a harkar yaɗa labarai.

Da yake mayar da martani, Kwamishina Waiya ya yi maraba da ziyarar, inda ya bayyana shirinsu na ɗorewar haɗin gwiwa a tsakanin ɓangarorin biyu.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS