Gwamnatin Kano ta haramta amfani da littafin ‘Queen Primer’ saboda lalata tarbiya

Amfani da kalmar ‘gay’ wani sako ne da a wannan zamanin ake jingina ta ga ’yan luwaɗi.

Gwamnatin Kano ta haramta amfani da littafin ‘Queen Primer’ saboda lalata tarbiya

Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Kano ta haramta karantawa da sayarwa da duk wata mu’amala da littafin Queen Primer a fadin jihar.

Shugaban Hukumar, Abba El-Mustapha ne ya bayyana haka ranar Alhamis a yayin da ya jagoranci kwace kwafi-kwafi masu dimbin yawa na littattafan.

Bayanai sun ce littafin yana dauke da wasu kalaman turanci irin su ‘let’s gay’ wato ‘mu shakata’, sai dai wasu na ganin amfani da kalmar ‘gay’ wani sako ne na lalata tarbiyyar jama’a da a wata fassarar ake jingina ta ga ’yan luwaɗi.

El-Mustapha ya ce littafin wanda ke koyar da rubutu da karatu a harshen Ingilishin yana yada ‘fasadi.’

Littafin Queen Primer
Wani shafi daga cikin littafin Queen Primer mai dauke kalmar gay da aka fi alakanta wa da masu luwaɗi.

“Littafin yana cike da maganganu na fasadi wadanda ba su kamata a ce ’ya’yanmu sun ji su ba kuma an karantar da su ba,” in ji shi kamar yadda ya wallafa a wani bidiyo a shafinsa na Facebook.

Shugaban hukumar ya ce jami’ansa sun kama kwafin littafin guda 1,200 daga kasuwannin da ake sayar da su.

Kazalika ya ce za su ci gaba da bincike a kan al’amarin kuma ya sha alwashin gurfanar da duk wanda aka sake kamawa yana sayar da littafin a gaban kuliya.

“Matsayar wannan hukuma ita ce dakatar da sayar da wannan littafin da dangoginsa. Kuma ta hana amfani da shi a cikin [jihar] Kano gaba daya.

“Sannan duk wasu makarantu da ke koyar da yara wannan littafin daga yanzu mun hana. Kuma mun haramta sayar da shi gaba daya a jihar Kano,” in ji Abba El-Mustapha.

Aminiya ta ruwaito cewa, Bajimin malamin nan na addinin Islama kuma Babban Limamin Masallacin Al-Furqan da ke Unguwar Nasarawa a Kano, Dokta Aliyu Bashir, na daya daga cikin wadanda suka soma ankarar da al’umma kan hadarin da ke tattare da sabon kwafin littafin na.

Lamarin dai ya jawo ce-ce-ku-ce a ’yan kwanakin nan musamman a kafafen sada zumunta, inda masu fada a ji da hangen nesa ke ci gaba da gargadin littafin da ake amfani wajen koyar da harshen Turancin Ingilishi ga yara ’yan reno na nazare da firamare na dauke da wasu kalmomi na lalata tarbiya.

Gwamnatin Kano ta dauki mataki kan wasu littafan

Kazalika, Gwamnatin Kano ta dauki matakin haramta amfani da wasu littafan kan abin da ta ce suna dauke da bayanai na jima’i da sauran dangogin na batsa.

Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai bai wa Gwamnan Kano shawara ta musamman kan makarantun gwamnati da masu zaman kansu, Kwamared Baba Abubakar Umar ya fitar ranar Alhamis.

Sanarwar ta ja hankalin dukkan masu ruwa da tsaki da su kauracewa amfani da littafan da ke dauke da sakon bayyana jima’i karara da lalata tarbiyar dalibai.

Jerin littafan da sanarwar ta ce sun haramta sun hada da:

Queen Primer tun daga kan tsohon bugu har sabo.

Basic Science for Junior Secondary bugun 2018 wanda Razat Publishers ta wallafa (JSS3).

Active Basic Science, bugun 2014, wanda Tola Anjorin da Okechukwu Okola da Phillas Yara da Bamidele Mutiu da Fatima Koki da Lydia Gbagu suka wallafa.

Basic Science and Technology for Junior Secondary School, na 1, 2 da na 3, wanda W. K Hamzat da S. Bakare suka wallafa.

New Concept English for Senior Secondary Schools for SS2, sabon bugun na shekarar 2018, wanda J Eyisi da A Adekunle da T Adepolu da F Ademola Adeoye da Q Adams da J Eto suka wallafa.

Basic Social Studies na makarantun firamare, wanda B J Obebe da D M Mohammed da S N Nwosu da J A Adeyanju da H Carbin suka wallafa.

MURIC ta yaba wa Gwamnatin Kano 

Tuni dai Kungiyar Kare Hakkin Musulmi a Najeriya (MURIC) ta yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bisa hana ta’ammali da wadannan littafan a makarantun reno, firamare da sakandare saboda shigar da wasu bayanai da suka shafi jima’i.

Shugaban MURIC reshen Jihar Kano, Mista Hassan Indabawa, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce matakin da gwamnati ta dauka na cire wasu gurbatattun kayan koyarwa daga cikin manhajar makarantun firamare abin yabawa ne.

Ya ce matakin Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Yusuf ya zo a daidai lokacin da ya dace.

Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara

Turmutsutsun abinci: Najeriya na fuskantar annobar yunwa – LP

An yanke wa direba hukuncin kisa kan kashe mutum 35 a China

Lalacewar jirgin ƙasa ya sa fasinjoji sun maƙale a Delta